
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Amurka ta yaba wa Nijeriya bisa hanzarta aiwatar da shari’o’in da suka shafi ta’addanci a ƙasar, bayan an yanke hukunci akan mutane 386 da ake zargi da hannu a ayyukan.
A wata sanarwa daga babban mai bada shawara na Amurka akan harkokin Afirka da Larabawa, Massad Boulos ya fitar, ya ce wannan mataki na nuna ƙoƙarin ƙarfafa adalci da riƙon amana a tsarin shari’a, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Ya jaddada cewa gudanar da shari’a cikin gaggawa da gaskiya na da muhimmanci wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da kuma tabbatar da tsaron ƙasa.
Haka kuma, Ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya bayyana cewa an samu waɗannan hukuncin ne daga cikin shari’o’i 508 da aka gabatar akan mutanen.
Gwamnatin Tarayya na cigaba da ƙarfafa matakan yaƙi da masu daukar nauyin ta’addanci, inda aka fitar da sunayen mutane da kungiyoyi guda 48 da ake zargi da hannu a ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Nijeriya.
Kaɗan daga cikin sunayen sun haɗa da Simon Ekpa, Tukur Mamu, da kuma ƙungiyoyi kamar su IPOB, Ansarul Sudan da ISWAP da ke ayyukansu a Arewa maso Gabashin Nijeriya da wasu sassan ƙasar.
