Sojoji sun kama ɗan shekara 15 da aka danganta da kisan birgediya janar a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai sun yi ram da wani matashi mai kimanin shekaru 15 bisa zargin sa da hannu a kisan wani mummunan hari da aka kai a Jihar Borno.

Matashin mai suna Tijjani Madu ya shiga hannun jami’an tsarin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa siyo abinci ga sauran ‘yan uwansa ‘yan ta’adda.

Wata majiya mai ƙarfi ta ce, ana zargin sa da hannu a harin da ya yi sanadiyyar mutuwar Birgediya Janar Oseni Braimah da wasu dakaru da dama.

A ranar Alhamis aka ƙaddamar da harin a wani sansanin soja, inda ake zargin mayaƙan Boko Haram da hannu a ciki.

Matashin ya bayyana cewa ya taɓa shiga hare-hare a Benisheik da Ngamdu da ya yu ajalin dakarun tsaro masu yawa.

Sannan, an cika hannu da shi ne a lokacin da aka tura shi daga Jilli da kuɗi kimamin N850,000 domin sayen kayan aiki.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su fitar da cikakken bayani a hukumance ba game da al’amarin.

By Babaji