Amurka ta rasa mafakarta ta mai kare haƙƙin bil Adama a 2021

Daga CRI HAUSA

Sakamakon binciken ra’ayin jama’ar Amurka da aka fitar a kwanakin baya, ya nuna cewa, sama da rabin Amurkawa suna mayar da shekarar 2021 a matsayin shekara mafi wahala, lamarin da ya shaida cewa, yanayin kare haƙƙin bil adama da Amurka ke ciki ya ƙara tsananta.

Da farko, gaza daƙile yaɗuwar annobar cutar COVID-19 ya jefa al’ummun ƙasar ta Amurka cikin mawuyacin hali. A shekarar 2021, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar suka kamu da cutar a Amurka ya kai miliyan 34.51, kuma adadin mutanen da suka rasa rayuka sakamakon cutar ya kai dubu 480, adadin da ya kai sahun gaba a duniya. Ana iya cewa, dalilin hakan shi ne ‘yan siyasar Amurka, sun yi watsi da lafiyar al’ummun ƙasar, tare da siyasantar da annobar.

Kana sakamakon binciken ya nuna cewa, matasan Amurka kaso 7 bisa ɗari kacal ne ke ganin cewa, Amurka tana gudanar da tsarin demokuraɗiyya yadda ya kamata.

Haƙiƙa a shekarar 2021, Amurka ta rasa mafakarta ta kasancewa mai kare haƙƙin bil adama, gwamnatin Amurka ta nuna wa al’ummun ƙasa da ƙasa yadda take rasa kimar “haƙƙin bil adama mai salon Amurka” ta hanyar ɗaukar haƙiƙanin matakai. Misali kan hakan akwai tashin hankalin da ya faru a babban ginin majalisar dokokin ƙasar a watan Janairu, da janyewar sojojin ƙasar daga Afghanistan a watan Agusta, da gaza samun sakamako yayin taron kolin demokuraɗiyya a watan Disamba.

An lura cewa, ma’anar “haƙƙin dan adama” a zukatun ‘yan siyasar Amurka ita ce, “nuna fin ƙarfi”. Don haka, ƙasashen duniya da dama a yayin taro karo na 48 na majalisar kare haƙƙin bil adama ta MDD da aka kira a shekarar 2021 ke cewa, Amurka ƙasa ce mai gurgunta sha’anin kare haƙƙin bil adama na duniya. (Mai

fassarawa: Jamila