Sin ta yi maraba da shawarwarin Ukraine da Rasha

Daga CRI HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata cewa, ƙasarsa tana goyon bayan duk wani yunƙuri na diflomasiyya da zai taimaka wajen warware rikicin ƙasar Ukraine cikin lumana, kana tana maraba da ƙaddamar da shawarwarin zaman lafiya tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, a matsayin martani ga shawarwarin da tawagogin ƙasashen Rasha da Ukraine suka gudanar a yankin Gomel na ƙasar Belarus jiya Litinin.

Wang ya ƙara da cewa, ƙasar Sin na fatan ɓangarorin biyu za su ci gaba da yin shawarwari da neman hanyar siyasa wajen warware matsalolin tsaro na ɓangarorin biyu, da tabbatar da tsaron bai ɗaya a nahiyar Turai, da kuma samar da dauwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Turai.

Fassarawa: Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *