An ɗaure ɗan sanda da ya sace kuɗin lalitar da ya tsinta

An yanke wa wani tsohon ɗan sanda mai suna Mohammad Ghalayini hukuncin ɗaurin watanni 22 a gidan yari bisa samunsa da laifin satar Naira 36,000 (Fam 80) a wata lalitar da ta ɓata da aka miƙa ga ’yan sanda.

A cewar rahotannin BBC a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2022, an samu Ghalayini da laifin sata da kuma karkatar da tsarin shari’a bayan da wani ɗan sanda ya kai rahoton vacewar kuɗaɗen a watan Satumba, sannan aka ɗaure shi a watan Oktoba.

Ba a ba shi izinin yin aiki ga ‘yan sanda, hukumomin ’yan sanda na gida, Ofishin ‘Yan Sanda mai zaman kansa ko kuma ko wane hukuma ba.

“Ayyuka irin wannan a zahiri suna lalata kwarin gwiwa ga ‘yan sanda”, inji Babban Sufeto Caroline Haines.

Wani ma’aikacin kamfanin na Met ne ya ruwaito wannan satar wanda ya gano cewa fam 80 ne a cikin lalitar.

DC Haines, wanda ke da alhakin aikin ’yan sanda a yankin Arewa wanda ya haɗa da Haringey da Enfield, ya ce, “PC Ghalayini, bayan xaurin da aka yi masa, a yanzu haka an sallame shi ba tare da an sanar da shi ba sakamakon rashin gaskiya da yaudarar da ya yi.

“Yana da matuƙar muhimmanci mutane su ƙara amincewa da mu, amma ayyuka irin wannan suna lalata kwarin gwiwa ga ’yan sanda. Ƙoƙarinmu shine mu yi aiki don kawar da waɗanda ke lalata mu da cin mutuncin jama’a.”

A wani labarin kuma, Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) sun kwace wasu maƙudan kuɗaɗen waje daga hannun ’yan Nijeriya a tashoshin jiragen sama.

Daraktan Ayyuka, Abdulkarim Chukkol ne ya bayyana haka a shirin Barka da Safiya Nijeriya a gidan talabijin na NTA, a ranar Laraba, 16 ga Nuwamba, 2022.

Chukkol ya ce, badaqalar kuɗaɗen ne ya sa aka kama wasu ma’aikatan ofishin na BDC kwanan nan a Legas da Abuja.

A cewarsa, samamen da aka yi wa masu yin kisa a kasuwar a layi ɗaya ba wai kawai ba ne, illa dai na hankali ne.

Ya ce, “an kama mutane da yawa na masu fasa-kwaurin kuɗi tare da kwato maƙudan kuɗaɗen ƙasashen waje.

“An kama wasu da sama da dala miliyan 6, wasu da dala miliyan biyu.

“Mun san cewa waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba na amfani bane wajen da sayen kaya, an wawure kuɗaɗen ne don sata.”

Chukkol ya tabbatar da cewa hukumar EFCC ta kwace kuɗaɗen p ga gwamnatin tarayya tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.