Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar masu zuwa Amurka da Birtaniya su yi hattara da ɓarayi

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Nijeriya ta shawarci ’yan ƙasar da su zama masu kula da kayansu sosai duk lokacin da suka tashi tafiya zuwa ƙasashen Amurka da Birtaniya da sauransu, gudun faɗawa tarkon barayi.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammad ne ya yi wannan gargaydi ran Litinin a Abuja.

Ministan ya ce abin damuwa ne ganin yadda ’yan Nijeriya masu zuwa Amurka da Birtaniya da sauransu, ke faɗawa tarkon ɓarayi inda suke sace musu kudi fasfo.

Ya ce, “Waɗanda abin ya shafa a baya-bayan nan su ne waɗanda suka tafi Birtaniya wanda akasarinsu aka sace musu kayayyakinsu a manyan shaguna, musamman a babban titin Oxford.

“Don haka muka yanke shawartar ’yan Nijeriya masu zuwa Birtaniya da Amurka da su zamo masu kula da kayayyakin sosai don kada a raba su da su,” inji shi.