Matashi ya nemi kotu ta hana iyayen budurwarsa aurar da ita

Wani matashi ya yi ƙarar iyayen budurwarsa a gaban Babbar Kotun Shar’iar Musulunci da ke Hotoro a Kano yana neman kotun ta hana su aurar da ita ga wani matashi daban.

Tunda farko matashin mai suna Imam Mukhtar Dala ya yi ƙarar budurwarsa Muhasin Auwal Dala da mahaifinta A.A. Dala da kakanta Sani Mai Alawayyo da kuma aminin babanta, Alhaji Audu, inda ya nemi kotu ta dakatar da auren da ake ƙoƙarin yi wa Muhasin ɗin saboda shi ne ya yi hidimar da zai aure ta.

Haka kuma ya nemi a hana Muhasin Dala zuwa wurin kowane mutum don ɗaura mata aure.

A zaman kotun lauyoyin waɗanda ake ƙara ƙarƙashin jagorancin Barista Muhammad Lagazan Abubakar suka nemi kotun ta cire sunan wasu daga cikin shari’ar da suka haɗa da kakan yarinyar Alhaji Sani Mai Alawayyo da kuma aminin mahaifinta Alhaji Audu kasancewar ba su da hannu a cikin shari’ar.

Barista Lagazan ya nemi kotun ta ba shi dama ya yi martani da baki sai dai kotun ta qi amincewa da buƙatarsa, inda ta dage cewa a rubuce ake buƙatar martanin nasa.

Shi ma lauyan wanda ya yi ƙarar, Barista Mujiburrahman Ahmad ya nemi kotun ta ba shi lokacin yin nazari don mayar da martani game da buƙatar lauyoyin waɗanda ake ƙara na janye wasu daga cikin shari’ar.

Alƙalin Kotun Mai shari’a Isa Salisu Kura ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga Nuwamban nan.