An binne gawar marigayi Janar Muhammadu Buhari a gidansa dake Daura a Jihar Katsina

Spread the love

Jana’izar marigayin ta samu halartar Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, shugaban ƙasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló, da Fraministan Ministan Jamhuriyar Nijar, Ali Lamine Zeine.

Sauran manyan baki sun haɗa da shugabannin rundunonin tsaro, shugabannin masana’antu, Ministoci, tsofaffin gwamnoni, wakilin shugaban ƙasar Chadi, malamai, da fitattun mutane daga cikin gida da waje. Kafin binne gawar, dakarun haɗin gwiwar sojoji sun gudanar da harbe-harben ban girma sau 21 a matsayin girmamawa ta ƙarshe ga marigayin.

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, shi ne ya karanta tarihin rayuwar Buhari a taron, inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Najeriya da iyalansa.

Ya ce, marigayin soja ne na gari mai ƙwazo, gaskiya, da kishi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar ƙasa da kyakkyawan shugabanci.

A lokacin da aka iso Daura da gawar, dubban jama’a ne suka taru suna kabarbari da addu’ar rahama ga marigayin. Iyalansa sun samu damar duban gawarsa na ‘yan mintoci kaɗan don yin addu’ar karshe kafin a rufe shi kabarinsa.

Marigayi Muhammadu Buhari ya shugabanci Nijeriya a matsayin shugaban soja daga 1984 zuwa 1985, sannan ya sake komawa mulki ta hanyar zaɓe a 2015, kuma aka sake zaɓarsa a 2019.

Mulkinsa ya shahara da yaƙi da cin hanci, manyan ayyukan raya ƙasa, da kuma fuskantar ƙalubale a fannonin tsaro da ci-gaban tattalin arziƙi.

By Babaji