“Duk marubucin da ya shahara za ka same shi mai yawan karatun na wasu ne”
Daga AISHA ASAS
Shugaban ɗaya daga cikin ƙungiyoyin marubuta da suke fafutukar ganin sun inganta sha’anin rubutun Hausa, Sani Shehu Lere, jajirtaccen marubuci kuma shugaban ƙungiyar Mikiya Hausa writers da ke Jihar Kaduna, ya samu damar amsa tambayoyin shafin Adabi na jaridar al’umma Manhaja. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
MANHAJA: Mu fara da jin tarihinka.
SANI LERE: Sunana Sani Shehu Lere. An haife ni a cikin garin Lere ta ƙaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.
Na yi makarantar firamare a Gyaɗi-Gyaɗi ‘Special Primary School’ a garin Kano. Sa’annan na yi makarantar gaba da firamare a Ahmad Muhammad Maƙarfi da ke garin Kaduna. Sannan na kammala digiri na farko a jami’ar Jihar Kaduna (KASU), inda na karanci Hausa.
Na yi karatun addinin Musulunci gwargwadon hali, na sauke Alƙur’ani mai girma tare da ilimin Hadisi, Fiƙihu da kuma tarihi. Na yi aure, ina da ‘ya’ya shida, huɗu mata, biyu maza.
Ina da sha’awar shiga duk wata harka da ta shafi gwagwarmaya don yin faɗa da zalunci, don tabbatar da adalci, wannan ta sa ni shiga ƙungiyoyin gwagwarmaya daban-daban tun daga ta ɗalibai da ta jama’ar gari. Ina son tufafi launin kore, ina kuma son doya da kuma tuwon shinkafa miyar ganye a cikin abinci. Ina son mace mai kunya mai yawan sa hijabi.
Ko za mu iya sanin sunayen litattafan da ka wallafa?
Na rubuta littafai masu dama, sai dai guda ɗaya ne na samu damar buga wa har ya shiga kasuwa, saboda irin matsalolin da kasuwar littafai ta tsinci kanta na tsakanin mawallafa da masu dillancin littatafan, wato “kura da shan duka, Gardi da karɓar kuɗi.” Littafin da ya samu shiga kasuwa kuwa shine, ‘Aiki Ja’. Waɗanda kuma suke a rubuce ba su samu shiga kasuwa ba sun haɗa da;
‘Na barshi da Allah’, ‘Soyayya Ta Hanyar Internet’, ‘Burin Mamaci’, ‘Gidan Kaso’ da sauransu.
Me ya ja ra’ayinka ga harkar rubutu?
Kamar yadda kowa ya sani, rubutu wata hanya ce ta aika saƙon da ke zuciya zuwa ga al’umma, wato kowanne marubuci a kwai dalilin da kan tsunduma shi cikin harkar rubutu, galiba ya kan tsinci kansa ne a wani yanayi ko dai na farin ciki ko kuma na baƙin ciki, amma galiba na baƙin cikin sun fi yawa, da yake ɗaukar hanyar rubutu ta zame masa hanyar da zai bayyana wa duniya halin da yake ciki, ko don ya zama izna ko darasi ko kuma shimfiɗa ga ‘yan baya.
Haƙiƙa ni gwagwarmayar yaƙi da zalunci da ƙoƙarin ganin an yi adalci shi ne sila na tsunduma ta cikin harkar rubutu. Littafi na na farko wato ‘Aiki Ja’ labari ne da ke nuna wa mai karatu yadda a ke jajirce wa da ɗaukar duk wata tsangwama da cutarwa a yayin da kake aiwatar da wani abu da ka san mai kyau ne, kuma mai amfani ga al’umma, ko da kuwa ya zame wa mutane wani sabon abu wadda ba su fahimce shi ba, ka daure ka ci gaba har akai lokacin da za a fahimce ka. Kamu da kisan da marigayi Janar Sani Abacha ya yi wa ‘Muslim Brothers’ da sanya ƙarfi fiye da ƙima a kan su ta sanya ni shiga cikin mutanen da suke ganin bai kamata a yi amfani da makami mai kisa a kan fararen hula ba. Idan kuma har ɗaukar matakin yin hakan ya zama dole, to a kama ne a kai wa Kotu ta yanke hukunci ba a ɗauki doka a hannu ba ‘eɗtra judicial killing’. A dalilin wannan gwagwarmaya ne ta sa na yi sha’awar rubuta littafin da ya ƙunshi manufata da saƙon zuciyata ga al’umma a cikin labari, a taƙaice wannan shine dalilin shiga ta harkar rubutu.
Wacce shekara ka fara rubutu?
Na fara rubutu ne a shekarar 1996 bayan kwaranyewar taƙaddamar ‘Muslim Brothers’ da Janar Abacha, amma ban samu buga wa ba sai a shekarar 2007.
Ka kasance shugaba na ƙungiyar marubuta, wato Mikiya Hausa writers’. Mene ne maƙasudin kafa wannan ƙungiyar?
Ni ne Shugaban ƙungiyar marubuta ta Mikiya Hausa Writers. Dalilin kafuwarta kuwa shi ne, kafin kafuwarta ina cikin ƙungiyar marubuta ta Alƙalami, wacce marigayi Mahmoon Baba Ahmad yake a matsayin ubanta mai bata tarbiyya. To bayan rasuwarsa, sai ƙungiyar ta shiga cikin matsanancin maraici na rashin uba mai tsawata mata, don haka sai ni da wasu daga cikin marubata masu kishin harkar rubutu irin su; Sani Ahmad Giwa, Aisha Asas, Anty Sa’adiyya Kaduna, Maryam Nadabo, Basira Sabo Nadabo, MD Asnanic, I. Kura, da waɗansu da dama, mu ka tattauna barin ƙungiyar tare da kafa wata sabuwa don ƙara haɓakar harkar rubutu da marubuta. Kuma alhamdu lillahi, daga kafuwarta zuwa yanzu an samu ƙarin marubuta da masu sha’awar rubutu da dama saboda kwasa-kwasai da ƙungiyar kan gudanar a kan harkar rubutu da taron ƙara wa juna sani daga lokaci zuwa lokaci.
Mene ne tasirin ƙungiyar marubuta ga marubuci?
ƙungiya a ko’ina take, tana da matuƙar amfani ga masu yin ta. A duk inda kaga mutane sun haɗu sun samar da ƙungiya, za ka samu suna da tunani iri ɗaya, kuma nasarar da suke so su samu iri ɗaya ce, sai su haɗa hannu wuri ɗaya don kai wa ga muradin da in mutum ɗaya ne zai yi masa wahalar isa gare shi, shi ya sa a ke cewa, ‘ƙungiyar taimakon kai da kai’.
To ƙungiyar marubuta ma bata sauya daga irin nau’in ƙungiyoyi ba, sai dai ta sauya ta fannin manufa. Shiga ƙungiyar marubuta ga marubuci ba ƙaramin tasiri take da shi ba domin tana haifar masa da alfanu masu tarin yawa kamar; Ba shi damar haɗuwa da marubuta na nesa da kusa tare da sanin juna. Ba shi damar goge wa da samun ƙarin fasahohi daga rubututtukan wasu. Ba shi damar gyara kura-kurai da sanin ƙa’idojin rubutu daga tarukan ƙara wa juna sani da ƙungiyoyi kan shirya wa marubuta. Samun sauƙin buga littafi da tallata shi a ƙarƙashin ƙungiya don guje wa haɗarin dillancin littattafai da akan samu a yawancin lokuta. A kwai tasiri da alfanu masu tarin yawa waɗanda marubucin da yake cikin ƙungiya zai samu.
Wane lokaci ka fi sha’awar yin rubutu?
Ni a kodayaushe ina yin rubutu matuƙar wani abin da ya dace da rubutu ya faru. Shi rubutu kan zo ne a yayin da buƙatarsa ta zo, galiba ba shirya masa a ke ba, zuwa yake yi. Kamar yadda na yi bayani a baya, wani hali za ka shiga ko tsaka-mai wuya da zai tilasta ma ka yin rubutu a kan sa, domin duniya ta ji muryarka, to a she kuwa, yanayin ka iya canza wa daga lokaci zuwa lokaci. Sai dai na fi sha’awar rubutun a lokacin dare lokacin da babu hayaniya, domin ƙwaƙwalwa tafi samun zarafin yin tunani mai zurfi a wannan lokacin.
Kenan marubuci ba shi da damar gayyato rubutu a lokacin da yake buƙatar yin sa, sai dai rubutun ya zo a lokacin da wani abu ya samu marubucin ko ya ba wa marubucin damar yi?
Eh, a fahimtata rubutu ba ya samu wa sai an sami abin rubutawa. Ai rubutu hira ce da zuciya, saboda haka, baza ka iya rubuta abin da zuciyarka ba ta yi ƙuduri ba, samuwar ƙudurin a zuciya shi ne tushen rubutu.
Abin da na ke nufi da faruwar abu shi ne, idan salon rubutunka kan ginu ne bisa abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma na yau da kullum, to za ka rubuta bayan faruwarsa ko kuma a tunanin hasashen faruwarsa a nan gaba, to kuwa zuwan tunanin shi a ke nufi da samun abin rubutawa.
Sau da yawa, a kwai rubuce-rubuce da suka shafi almara, a kan kawo wasu abubuwan da ƙila babu su a zahiri, ko kuma a kawo abin da ya zarta tunani, to wannan duk sakamakon tunanin marubuci ne, a nan, tunanin da ya tunano masa waɗannan surkullen, su suka haifar masa da abin rubutu.
Masana ilimin fassara, sun jero ƙa’idojin samu ko yin fassara daga wani harshe zuwa wani da cewa; Farko dai dole a sami harshen da a ke buƙatar a fassara da kuma harshen da a ke so a fassara zuwa gare shi. Abu na biyu kuma, dole a sami abin fassara wa kamar rubutu ko magana ko alama ko nuni. To haka shi ma rubutu baya samuwa sai an sami Jigon da ake buƙatar yin rubutu a kai, matuƙar babu to babu rubutu. Shi kuma jigo kan zo ne bisa tunani ko faruwar wani al’amari, matuƙar babu wannan to babu rubutu.
Za mu so jin nasarorin da rubutu ya ba ka?
Na sami nasarori a harkar rubutu masu yawa, domin harkar rubutu ta tallatani duniya ta sanni. Sau da yawa na kan sami kiran waya daga masu karatu daga ciki da ƙasashe maƙobta. Kinga ashe da badon rubutu ba da ba su sanni ba balle su yi sha’awar sada zumunci da ni. Sa’annan kuma, dalilin rubutu na sami alaƙa ta kusa da wasu fitattun marubuta kamar; Marigayi Mahmoon Baba Ahmad da Marigayi Madu Iro da Marigayi Dr. Junaid, kuma na sami ƙaruwa da tagomashi sosai kafin Allah ya karɓi rayukansu. Allah Ya jiƙan su.
Ka fuskanci ƙalubale?
Eh, dole ne a dukkan lamari akwai nasara, akwai ƙalubale, amma ƙalubalen da na fuskanta a harkar rubutu bai wuce yadda karatun littafi ya koma gun mata ba, su kuma matan ba sa buƙatar leƙa littafin da namiji ya yi balle ma su amfana da abin da ke ciki.
Zuwan marubuta a yanar gizo wato ‘online writers’ cigaba ne ko ci baya?
To mu na iya kiransa cigaba, domin duk lokacin da kiɗa ya canza to sai ayi maza a sauya rawa. Yanzu zamani ne na amfani da soshiyal midiya, don haka masu sha’awar rubutu waɗanda galiba ba su ƙware ba suka yi wa abin shigar sauri, a yayin da su marubuta na gaskiya suka koma gefe suna nuna ƙyama. Kamata ya yi marubuta littafi su shigo cikin harkar rubutun soshiyal midiya don dusashe hasken gurɓatattun marubuta.
Ta ya marubuciya zai iya bada gudunmawa ta ɓangaren siyasa?
Ai shi marubuci ɗan rahoto ne, to kuwa kaga matuƙar ba a iyakance wa ɗan jarida iyaka ba wajen ɗauko rahoto, to haka shi ma marubuci.
Marubuta na iya bada gagarumar gudunmawa wajen gyaruwar siyasa da ba wa shugabanni shawara, da wayar da kan talakawa a ɓangaren abin da ya shafi al’amuran zaɓe da kuma shugabanci. Littafin ‘Dambarwar Siyasa’ da kamfanin jaridar Aminiya ya ɗauki nauyin bugawa babbar misali ne na irin gudunmawar marubuta a ɓangaren siyasa.
Wacce hanya ce kake ganin gwamnati za ta iya tallafa wa marubuci?
Akwai hanyoyi da dama da gwamnati zata iya tallafa wa harkar rubutu da kuma marubuta kamar; ƙarfafa Hukumar Tarihi da Raya Al’adu da samar mata da isasun kuɗaɗe don shirya tarukan ƙarawa juna ilimi ga marubuta, ɗaukar nauyin buga littafan da tallatasu, samar da basussuka masu sauƙin ruwa. Idan aka sami wannan daga gwamnati tabbas harkar rubutu za ta ƙara haɓaka.
Wasu na ganin rashin samun agajin gwamnati na daga cikin dalilan yawaitar matsalolin marubuta Hausa. Shin mene ne za ka iya faɗa a na ka mahangar?
Eh, haka ne. Domin an wayi gari da yawa daga marubuta sun bar rubutu ba kuma don babu basirar yin rubutun ba ne, sai kawai don idan ka zuba kuɗinka uwar kuɗi baza ta dawo ba balle a yi tunanin riba, saboda babu ingantattar harkar dillancin littattafan kuma babu wani tallafi daga gwamnati, shi yasa a kullm adadin littattafan da a ke samarwa ƙara ƙasa yake kullum rana.
Rubutun batsa na ɗaya daga cikin ci bayan da rubutun malam Bahaushe ya samu. A ganinka, me ya jawo yawaitar sa?
Yawaitar rubutun batsa ya yawaita ne a shafukan sada zumunta (online writers) dalili kuwa, saboda galiba irin ɗabi’un matasan wannan zamani kenan, abin da suka fi so kenan, don haka idan har kana buƙatar samun mabiya da yawa cikin ƙanƙanin lokaci to ka surka da batsa. Abin da ya haifar da haka kuwa shine, rashin ƙaidi a harkar ‘Intanet’, wato wata mahaɗa ce da ba ta da linzami, linzamin ta su ne iyaye da malamai da kuma gwamnati wajen haɗa hannu don yaƙar wannan musiba.
Wacce shawara za ka ba wa marubuta masu tasowa?
Shawarata ga marubuta masu tasowa itace, su yi ƙoƙarin yin mu’amala da tsoffin marubuta don samun shawarwari da kuma ɗora su bisa turbar da zata taimaki rubutunsu ya zama mai amfani garesu da ƙasarsu da kuma al’umma. Su kuma guji yin rubutun da ba shi da amfani wajen gyara tarbiyya da al’adu don kawai neman kuɗi, su yi rubutun da zai sa a riƙa karantawa ana yi mu su kyakkyawar addu’a kamar yadda mu ke karanta littattafan Alhaji Abubakar Imam da sauransu mu ke yi mu su addu’a.
Ya kake samun jigo idan za ka yi rubutu?
Ni a wurina samun jigo ba ya bani wahala, faruwar abin da ya dace in yi rubutu a kai shi ne jigona. Salon rubutuna ya sha bambam da salon wasu marubuta. Ni ban mai da hankali a kan rubutun soyayya zalla ba, abin da ke faruwa a cikin al’umma na yau da kullum shi nafi mai da hankali na a kai, don haka samuwar abu sabo a wurina shi ne jigo na.
Ta ya kake ganin marubuci zai inganta rubutunsa?
Marubuci zai inganta rubutunsa ne kaɗai ta hanyar karanta rubutun wasu. Duk marubucin da ya shahara, to za ka same shi mai yawan karatu ne, a yayin da ka karanta rubutu masu yawa, idan ka tashi yin naka zai inganta, amma ba zai yiwu ka ce kana son ka zama ƙwararren marubuci ba tare da yawan karatu ba, duk marubuci makaranci ne, amma ba kowanne makaranci ne marubuci ba.
Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.
