Ilimi na samun cigaba a gwamnatin Abba Kabir – Ahmad Dawaki

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An bayyana yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samar da kayan koyo da koyarwa a makarantun dake ƙananan hukumomin jihar nan 44, wanda hakan ba ƙaramin sauyi ya kawo ba a harkokin karatu a jihar nan.

Sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ahmad Shu’aibu Dawaki shi ne ya bayyana haka yayin da yake ƙarin haske dangane da cigaban da aka samu ta ɓangaren ilimi a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Sakataren ilimi ya bayyana cewa kayan koyo da koyarwa da Gwamna ya raba a makarantun faɗin jihar nan, wanda ya ce, ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta ga cigaba mai yawan gaske ta fuskar inganta harkokin koyo da koyarwa a faɗin matakarantun yankin.

Ta cikin wata sanarwa da jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta rabawa manema labarai ta ce Alhaji Ahmad Shu’aibu ya ce, saboda yadda gwamna ya dawo da shirin samar da kayan makaranta ga ɗalibai da ciyar da malaman makarantu gaba, hakan ya ƙara taimakawa wajen ƙaruwar yawan ɗalibai da suke zuwa makaranta.

Ya kara da cewa “Eriyoyin da muke da matsalar ɗalibai da ba zuwa makaranta, amma zuwan mai girma gwamna da jajircewar ciyaman gaskiya yanzu kwalliya tana biyan kuɗin sabulu, musamman yanzu lokacin damina idan ka je wasu yankunan ba za ka samu yara 50 suna zuwa makaranta ba a wancan lokacin amma yanzu fa”.

Daga nan kuma Sakatren, ya bayyana ɗaukar malaman BESDA da aka yi aiki da samar da kujerun zama da gyara ajujuwa da suka lalace da kuma ƙara gina sababbin ajujuwa a makarantun yankin, ya nuna cewa shekaru biyu na Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kawo cigaban da ba a samu ba a gwamnatin da ta gabata.

“Mai girma gwamna ya samar da abubuwa muhimmai masu taɓa zuciya ta cigaban ilimi, musamman mai girma gwamna da ya samar mana da ma’aikata, ya ɗebi malamai har karo uku; akwai waɗanda tsohuwar gwamnati ta ɗiba ta tafi ta bar su ba albashi, mai girma gwamna ya ɗebe su ya ci gaba da ba su albashi, sannan mai girma gwamna ya ɗebi ƴan BESDA an mai da su cikakkun ma’aikata sannan an yi karo na uku wanda a halin yanzu sun yi jarabawa suna jiran ta fito, da mai girma gwamna ya mayar da su cikakkun ma’aikata”. In ji Ahmad Shu’aibu

Sannan ya yi kira da Alhaji Ahmad Shu’aibu ya yi kira ga iyayen yara dake yankin, da su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai da goyon bayansu, ya kuma tare da kuma shawarci su a kan su riƙa ziyartar makatarantun ƴa ƴansu domin ganin halin da suke ciki ta fuskar karatunsu.

By ukarofi