Yankin Daura ya yi rashin Uba – Kwamred Mai’adua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin rashin da yafi kowane rashi ga al’ummar yankin Daura da Jihar Katsina baki ɗaya.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi kwamred Nasiru Wada Mai’adua yayi wannan magana a garin Daura a hira da manema labarai bayan da ya halarci jana’izar Muhammadu Buhari.

“Mutuwa na kan kowa kuma babu wanda ya san lokacin da zai mutu, amma mu mutanen yankin Daura zamu daɗe muna jimamin wannan babban rashi,”inji Mai’adua.

Ya bayyana cewa Buhari ne ya sanya aka kara sanin ƙasar Daura a duniya,”bamu taɓa sanin shugabannin ƙasashen waje za su zo garin Daura sai gashi dalilin sa mun gan su”shugaban NULGE ya ce.

Mai’adua wanda ɗan asalin garin Mai’adua da ke yankin Daura ya bayyana wasu abubuwan alheri na cigaba da marigayi Muhammadu Buhari ya Kawo wa yanki.

Sun haɗa da jami’ar sufuri da kwalejin kimiyya da fasaha duk na gwamnatin tarayya da kuma gina manyan tagwayen hanyoyi na zamani a yankin musamman cikin garin Daura.

Sai yayi kira ga al’ummar yankin da ƙasa baki ɗaya su sanya marigayi Muhammadu Buhari cikin addu’a Allah yafe masa kurakuransa.

Kwamred Nasiru Wada Mai’adua yayi kira ga shugabanni a kowani mataki da suyi koyi da halayen marigayi na kwatanta gaskiya da riƙon amana wajan tafiyar da harkokin shugabancin su.

By ukarofi