Gwamna Buni ya ƙaddamar da gasar karatun Alqurani ta 2025

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da gasar karatun Alqurani ta matakin ƙananan hukumomi na shekarar 2025, tare da gudanar da addu’o’i ga marigayi, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Taron ya gudana ne ranar Talata, a ɗakin taro na Federal Polytechnic Damaturu, a ƙarƙashin hukumar ilimin Larabci da addinin musulunci ta jihar Yobe (AISEB), da haɗin gwiwar PLAN International, mai fafutika wajen bunƙasa ilimin yara.

Gwamna Buni, wanda Kwamishina a ma’aikatar ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha, Farfesa Bello Kawuwa ya wakilta ya bayyana gamsuwa da ayyukan hukumar tare da shan alwashin bunƙasa ayyukanta.

Gwamnan ya jinjina wa AISEB kan gudanar da addu’o’i na musamman domin marigayi shugaban ƙasa, a daidai lokacin makoki da umarnin addu’a da Gwamna Buni ya bayar a gudanar a faɗin jihar.

Har wala yau, an bada kayan tsafta 99 ga Almajirai, tare da bayar da kyaututtuka ga ɗalibai 300 da suka yi fice a makarantar Islamiyya/tsangayoyi da kuma ƙaddamar da gasar karatun Alqurani a ɗaukacin ƙananan hukumomi 17 na jihar.

A nasa jawabin, sakataren hukumar AISEB, Dr. Malam Umar Abubakar, ya bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da addu’o’i na musamman a duk matakan gasar a cikin ƙananan hukumomi.

Ya ce: “A kowane mataki na gasar a ƙananan hukumomi 17, za mu riƙa gabatar da addu’o’i na musamman ga marigayi shugaban ƙasa, kamar yadda Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni ya umarta.”

Kimanin ɗalibai 300 ne suka ci gajiyar kyaututtuka, wanda suka yi fice ne wajen haddar Alqurani maigirma da fahimtar ilimin addinin Musulunci.

By ukarofi