Buhari: RTEAN ta kirayi mambobinta su yi addu’a ga marigayi tsohon shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Motoci ta Ƙasa (RTEAN) ta yi alhinin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Musa Muhammad Maitakobi a wata takarda, ya yi jimamin rashin marigayin Shugaban, wanda ya bayyana a matsayin jagora na gari mai ƙoƙarin riƙo da gaskiya bisa jajircewa da sadaukarwa ga al’ummar ƙasa.

Ya kuma ce, Buhari mutum ne da ya kasance mai kishin ƙasa kuma jagora abin koyi wajen tsayuwa akan hidimta wa ƙasa da al’umma, yana mai cewa za a cigaba da tunawa da shi a zukatan al’umma.

A ƙarshe, ya yi kira ga miliyoyin mambobin RTEAN da ke baki ɗaya ƙananan hukumomin Nijeriya da sauran al’ummar ƙasa da su yi wa tsohon shugaban addu’ar fatan samun rahamar Allah.

By Babaji