Fethullah: Gwamnatin Turkiyya ta yi gargaɗin ɓullar sabuwar ƙungiyar ƴan ta’adda a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin ƙasar Turkiyya ta yi gargaɗin cewa akwai mambobin wata ƙungiyar ta’addanci da ake kira da ‘Fethullah’ a Nijeriya, waɗanda ke ayyukansu a ƙasar da wasu ƙasashe.

Jakadan ƙasar ga Nijeriya, Mehmet Poroy ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja, lokacin shagalin Ranar Dimukraɗiyya da Haɗin kai ta ƙasar.

Ambasada Poroy ya ce, akwai wata tawaga da ta yi yunƙurin juyin mulkin a Turkiyya a ranar 15 ga Yulin 2016, wanda ba a cimma nasara a kai ba, lamarin da aka zargi mayaƙan FETO da ƙaddamarwa.

Daga lokacin ne aka riƙa kama mambobin ƙungiyar a ko’ina a faɗin duniya, lamarin da acewarsa ya haifar da barazana ga al’umma a ƙasashe da dama duba da bazuwar da suka yi a wurare ciki har da Nijeriya.

Ya kuma ce, ta hanyar haɗin-gwiwa tsakanin ƙasashen duniya, Turkiyya ta yi nasarar katse hanyoyin gudanar da ayyukan ƴan ta’addar a ƙasashe masu yawa.

“Abin takaici, ƙungiyar FETO tana cigaba da gudanar da ayyukanta a Nijeriya, musammman a fannonin ilimi da kiwon lafiya.”

“Mu na sanar da abokanmu ƴan Nijeriya game da tsari da haɗarin wannan ƙungiyar, kuma mun kiraye su da su kasance masu sanya ido da kulawa”, inji Poroy.

By Babaji