
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Da dama daga cikin manyan ƴan siyasa da masu alfarma ne suka taru a garin Daura a ranar Laraba, domin halartar addu’ar Fidda’u ga marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a wani asibiti dake Landon.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya jagoranci tawagar, wadda ta haɗa da Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda da Babagana Umara Zulum na Borno inda aka yi wa mamacin addu’o’in neman samun rahamar Allah.
Suaran sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar; tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP Peter Obi; da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Haka kuma, a taron akwai tsohon gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, Darakta-Janar na NDLEA Brig. Janar Buba Marwa (rtd), Sarkin Daura HRH Faruk Umar Faruk, tsohon shugaban sojoji Tukur Yusuf Buratai da kuma tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami.
Bugu da ƙari, taron ya samu halartar tshohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, tsohon Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami, Sanata Abdulaziz Yar’adua, mataimakin gwamnan Katsina Faruk Joɓe, da tsohon darakta-janar na NIA Ahmad Rufa’i da dai sauransu.
