Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa na Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, jam’iyyar da ya taimaka wajen kafa ta, bayan kusan shekaru biyu yana cikinta. Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓar Jada 1 a Jihar Adamawa, wacce ke ɗauke da kwanan wata na ranar 14 ga Yuli, 2025, yana mai cewa matakin ya zama dole sakamakon yadda jam’iyyar ke tafiya yanzu.

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin PDP a 2019 da 2023, ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa ne saboda “bambance-bambancen da ba za a iya sasanta su ba” da kuma kaucewa ga manufofin asali na jam’iyyar. Ya ce ficewar tasa cike take da alhini, amma ya gode wa jam’iyyar bisa dama da goyon bayan da ta ba shi a tsawon shekarun siyasar sa.

Wasiƙar ficewar tasa ta samu karɓuwa daga wani jami’in PDP a matakin mazaɓa, Hammedoma Abubakar, a ranar da aka aike da ita. Wannan mataki na Atiku na ficewa daga PDP ya tayar da cece-kuce a siyasar ƙasar, musamman yayin da ake ta hasashen matakin siyasa na gaba da zai ɗauka gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi