An gudanar da addu’ar ukun rasuwar Muhammadu Buhari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima ya jagoranci zaman addu’ar uku da ya gudana a garin marigayi Muhammadu Buhari.

Sauran waɗanda suka halarci zaman addu’ar akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Gwamnonin Katsina da Borno.

Akwai tsaffin gwamnonin Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i da Peter Obi ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gaba ta.

Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Farouk Lawal joɓe da mai martaba sarkin Daura Umar Farouk Umar da manyan jami’an gwamnatin tarayya da na Jihar Katsina suma duk sun halarci addu’ar.

Manyan malamai da limamai na yankin Daura sun gudanar da addu’oi ga marigayi Muhammadu Buhari da addu’ar samun zaman lafiya a ƙasa.

Kafin gudanar da addu’ar tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya jagoranci ayarinsa zuwa kabarin marigayi Muhammadu Buhari inda suka gudanar da addu’oi neman ma masa afuwa da fatan Allah yafe masa kurakuraensa.

Da yake jawabi bayan kammala addu’ar, gwamna Dikko Raɗɗa ya godewa mataimakin shugaban ƙasa wanda ya wakilci shugaban ƙasa.

Haka kuma ya godewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya mutunta al’ummar Jihar Katsina ya zo da kansa tare da wasu shugabannin ƙasashen waje.

Dikko Raɗɗa ya kira ga sauran shugabanni da suyi koyi da halayen marigayi Muhammadu Buhari.

Mataimakin shugaban ƙasa a nasa jawabin ya bayyana rasuwar Muhammadu Buhari a matsayin rashi ne ba ma ga Nijeriya ba har da ƙasashen Afrika.

Yayi fatan Allah masa rahama yaba iyalan sa haƙuri da juriya na rashi da a kayi.

Kashim Shettima ya sanar da cewa bisa umurnin shugaban ƙasa Bola Tinubu, iyalan marigayi Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina da shi mataimakin shugaban ƙasa za su sake zama a gidan marigayi domin gudanar da addu’oi na musamman kafin tawagar gwamnatin tarayya su wuce Abuja inda a can ma za su cigaba da amsar gaisuwa.

By ukarofi