Atiku, El-Rufai da sauransu sun ziyarci kabarin Buhari

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun kai ziyara zuwa kabarin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a garin Daura, Jihar Katsina. Tare da su akwai wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Ziyarar ta gudana ne a ranar Laraba, inda suka tsaya domin yin addu’a ga marigayin. Sun bayyana alhini da jimami a kan rasuwar Buhari tare da fatan Allah Ya jiƙansa da rahama.

Marigayin Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, bayan fama da jinya. Ya taɓa shugabantar Najeriya a matsayin shugaban mulkin soja da kuma shugaban ƙasa a mulkin farar hula.

By ukarofi