Gwamnatin Kano ta fara bincike kan rasuwar ɗalibai a sakandiren Bichi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Ali Makoɗa, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wasu ɗalibai guda biyu a makarantar Government Boarding Secondary School, Bichi.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗaliban da suka mutu, Hamza Tofawa da Umar Dungurawa, sun samu rauni sakamakon wani hari da wasu ɗaliban makarantar suka kai musu inda su ka yi amfani da wani irin ƙarfe da ake kira “gwale-gwale”.

Ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi, Balarabe Ƙiru, ya rabawa manema labarai a yau Laraba.

A cewar sanarwar, Kwamishinan Ilimi, ta bakin sakataren dindindin na ma’aikatar, Bashir Muhammad, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa kowa ya samu haƙƙinsa.

“Daga abinda muka samu ya nuna cewa wannan aika-aikar ta biyo bayan wani hukunci ne da wasu manyan ɗalibai suka ɗauka da kansu don ladabtar da waɗanda suka mutu, bisa zargin sun aikata wani laifi,” in ji shi.

Kazalika sakataren dindindin wanda ya ziyarci makarantar tun kafin fitar da sanarwar, ya shawarci ɗalibai da su riƙa zama masu hankali tare da guje wa ɗaukar doka a hannunsu.

“Lallai ya kamata ku guji ɗaukar doka a hannunku, ku tabbatar da kai kowacce irin matsala ga hukumomin makaranta domin su ɗauki mataki da ya dace,” a cewarsa.

Sannan ya bayyana ta’aziyya ga iyalan mamatan, inda ya ce: “A madadin Gwamnatin Jihar Kano, ma’aikatar ilimi da al’ummar Kano, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda su ka rasu , tare da addu’ar Allah ya gafarta musu, ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus.”

Waɗanda aka kai wa harin sun haɗa da Hamza Idris mai shekara 19 daga ajin SS3B, Umar Yusuf mai shekara 18 daga SS2C, Ibrahim Ibrahim daga SS2B, da Aliyu M. Nasir daga SS2C.

Daga bisani, an tabbatar da mutuwar Idris da Yusuf a asibitin gwamnati na Bichi, yayin da Ibrahim da Nasir ke ci gaba da samun kulawar likitoci.

By ukarofi