An cire Ronaldo daga cikin ‘yan wasan Portugal da za su fafata da Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin Tawagar Ƙwallon Ƙafar Portugal Fernando Santos ya ce, Cristiano Ronaldo baya cikin ’yan wasan da za su fafata da Super Eagles ta Nijeriya a wasan sada zumunta a yau alhamis ba sobado yana fama da ciwon ciki.

Ɗan wasan mai shekaru 37, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, bai yi atisaye a ranar Laraba ba, saboda rashin lafiyar da ta faro cikin yanayi na cece-kuce da ake yi kan hirarsa da Piers Morgans inda ya caccaki Manchester United.

Tuni aka cire hotunan Ronaldo daga bangon filin wasan Manchester United wato Old Trafford a jiya Laraba, yayin da yake cewa sun zuciyarsa ce ta kaishi ƙungiyar da aka yi masa wulaƙanci alhali kuwa ya kammala komai don zuwa City, amma ya bi zuciyarsa zuwa United.