An fitar da sakamakon gasar rubutu ta Bashir Othman Tofa 2025

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Bayan kammala tantancewar da alƙalan gasar rubutu ta tunawa da Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa suka yi a ranar asabar 16 ga Agusta 2025; hukumar Kano Book Club da The Third Space suka bayyana zakarun gasar gajerun labaran Hausa da aka gudanar a tsakanin Marubuta.

 A yayin taron dai shugaban alƙalan gasar Malam Isma’il Bala ya bayyana labarin ‘Ilimi Kogi’ na Hamza Sadiƙ Adam a matsayi na 1, yayin da labarin ‘Kazar Amarci’ na Muntasir Shehu ya zama na 2, sai kuma ‘Yaro Masomin Babba’ na Hassana Abdullahi Hunkuyi ya zo na 3. 

Ga dai jerin labaran daga na ɗaya zuwa na 3, da takardar shaidar karramawa da kuma kuɗin da aka ayyana ba su.

1. Ilimi Kogi na Hamza Sadiƙ Adam na 1 N150,000

2. Kazar Amarci na Muntasir Shehu na 2 N100,000

3. Yaro Masomin Babba na Hassana Abdullahi Hunkuyi na 3 N50,000

Sauran labaran da suka tsallake mataki na ƙarshe sun haɗar da:

* Ribar Adabi na Rufa’i Abubakar Adam

* Wutar Kara na Lantana Ja’afar

* Budurwar Zuciya na Usman Ibrahim Ali

* Tsaka Mai Wuya na Madina Bala Hussaini

Sai dai ba a bayyana wanne labari ne na 4 zuwa na 7 ba, an dai karrama su ne dai kawai a wajen bayyana zakarun gasar .

Tun da farko, an fara gudanar da bita ga marubutan da suka samu nasara da misalin ƙarfe 11 na safe a kan rubutu da salo da sauran sigogin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai, kafin daga bisani da misalin ƙarfe biyu na rana aka gabatar da taron karrama marubutan.

Bayan kyaututtukan littattafan marigayi Bashir Othman Tofa da aka bai wa zakarun gasar, an karɓi lambar asusun ajiyar marubuta ukun farko domin tura musu goron gasar. Taron ya samu halartar babban hadimin marigayi Bashir Othman Tofa wanda ya wakilci iyalansa wato Alhaji Unguwar Gini da Farfesa Abdallah Uba Adamu da alƙalan gasar da sauran marubutan Hausa da na Turanci.

By ukarofi