
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da ganin watan 12 a kalandar musulunci, wato Dhul Hijjah.
Hakan ya nuna cewa za a yi salla babba a ranar 6 ga watan Yuni yayin da za a yi hawan arfa a ranar 5 ga wata.
Kotun Koli, ta sanar da hakan a ranar Talata, kamar yadda aka ruwaito a labaran Arab News.
Al’ummar musulmi da ke aikin hajji a wannan shekarar za su yi sallar Eid-el-Kabir a ranar 6 ga wata.
Haka kuma masarauta Saudiyya ta bada hutu ga ma’aikatan gwamnati da na ma’aikatu masu zaman kansu.
