
Daga BELLO A. BABAJI
Wata Babbar Kotun Tarayya a Kaduna ta umarci tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i da wasu mutane biyar da su biya Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin diyya na tsare wasu jagororin Adara a shekarar 2019 ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan tauye musu ƴancin ɗan-adam ne.
Alƙali Hauwa’u Buhari ta gabatar da hukuncin a yayin shari’ar da wani Awemi Dio Maisamari da wasu mutane takwas na ƙabilar Adara daga Kudancin Kaduna suka shigar, ranar Talata.
Kotun ta ce, El-Rufa’i ya kama su ne bisa wani shiri na raɗin kansa, don haka zai biya diyyar miliyan N900.
Haka kuma, ta sanya tarar miliyan N10 na dameji da ƙarin miliyan N10 na dameji na musamman akan ƴan sanda da Sufeton ƴan sanda da kuma kwamishinan ƴan sanda.
An shigar da ƙarar ne sakamakon tsare mutanen a shekarar 2019 bayan kisan da aka yi wa Dakta Raphael Maiwada Galadima, wanda shi ne sarkin mutanen Adara a lokacin.
