An gano mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya

Bincike ya sa an gano mutumin da ya fi duka mutanen duniya tsawon hanci, wanda tsawon hancinsa ya kai inci uku da rabi.

Shekara 10 ke nan bayan mutumin mai suna Mehmet Ozyurek mai shekara 71 ɗan ƙasar Turkiyya ya fara shiga Kundin Tarihi na Guinness a matsayin wanda ya fi kowa tsawon hanci a shekarar 2010.

An fara tabbatar da tsayin hancin Mehmet ne bayan da ya bayyana a shirin wani gidan talabiji na ƙasar Italiya, inda aka gwada tsayin karan hancinsa, inda ya kai kusan santimita 8.8, kamar yadda jaridar The Mirror ta rawaito.

Jaridar The Mirror ta ce, “tsayin hancin Mehmet ya kai santimita 8 da ɗigo 8 wanda ya yi daidai da inci uku da rabi, idan aka auna daga tsakanin idanunsa zuwa ƙarshen karan hancinsa.”

Tun a lokacin aka ba Mehmet lambar yabo na Kundin Tarihin Guiness, kuma har zuwa yanzu ba a samu wanda ya doke shi wajen tsayin hanci ba.

Yanzu dai Mehmet Ozyurek ya kare kambinsa na rayayyen mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya.

Amma mutumin da ya fi tsawon hanci a duniya a tarihi shi ne wani mai suna Thomas Wedders daga yankin Yorkshire na ƙasar Birtaniya.

Kundin Tarihi na Guiness ya nuna cewa tsawon hancin Wedders, wanda ya rayu a shekarun 1770, ya kai santimita 19 wato inci bakwai da rabi.

Saboda tsawon hancinsa, Wedders, wanda ke cikin ayarin wasu ’yan gambara kan zaga gari suna nuna wa mutane hancin nasa.