Yadda wani matashi ya sanya kansa a kasuwa

Daga WAKILINMU

Wani matashi mai shekara 26 ya sa kansa inda yake neman wanda zai saye shi a Kano.

Matashin mai suna Aliyu Na Idris, wanda ɗan asalin Jihar Kaduna ne, yana yawo ne a kan tituna a Kano, ɗauke da kwali da aka rubuta ‘wannan mutumin na sayarwa ne a kan Naira miliyan 20.’

Shi dai Aliyu, wanda ya shafe kimanin kwana biyar yana yawon neman wanda zai saye shi a garin Kano, ya shaida wa manema labarai cewa shi dai a da tela ne, matsin rayuwa ce ta sa yake son sayar da kansa miliyan N20, kuma da sanin iyayensa.

Ya ƙara da cewa, da farko sai da ya fara tallata kansa a Kaduna ko za a samu mai sayen shi, amma da ya ga ba a taya shi da kyau ba, sai ya wuce zuwa Kano ko zai dace a saye shi a kan farashi mai kyau.

Ya ce, “duk da cewa na samu waɗanda suka taya ni a kan Naira miliyan 10, miliyan biyar da dubu ɗari uku a Kano, amma ban sallama musu ba, saboda abin da suke son su biya bai kai abin da nake so ba.”

Matashin ya ce, shi tela ne a da can amma daga baya komai ya taɓarɓare masa saboda matsalar kuɗaɗe, ya rasa kwastominsa, ga shi kuma jarinsa ya karye.

A cewarsa, a halin yanzu ba shi da wani abin da zai iya dogara da shi, ballantana ya samu jarin da zai fara wata sana’a, shi ya sa ya yanke shawarar ya ɗora wa kansa ganye ko zai samu a saye shi a Naira miliyan 20.

An tambaye shi cewa shin mai yake son yi ne da Naira miliyan 20 ɗin da yake so a saye shi, inda ya ce , “zan ba wa iyayena Naira miliyan 10, in ba da miliyan biyar a matsayin haraji a jihar da aka saye ni, mutumin da ya tallata ni har aka saye ni kuma zan ba shi Naira miliyan biyu, ragowar miliyan uku kuma zan ba wa duk wanda ya saye ni ya ajiye a matsayin kuɗin kula da ɗawainiyata.”

A cewarsa, ya san zai rasa ’yancinsa idan aka saye shi, amma ya gwammace hakan kuma a shirye yake ya yi abin da iyayen gidansa za su sa shi.

Ya ƙara da cewa, idan ba a samu mai sayen shi a Kano ba zai tafi wata jihar ya ci gaba da tallata manhajarsa.