Me ya sa Ado Gidan Dabino ya ke mamaye kyautar jarumin jarumai?

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ba baƙo ba ne a masana’antar Kannywood da kasuwar adabi, domin su ne suka yanke wa Kannywood cibiya. Ya fara da dirama (wasan daɓe) ne tun a shekarar 1984, wato shekaru 37 da suka gabata. A zantawarsa da Wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji yadda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe kyautar jarumin jarumai har sau uku a shekara ɗaya kuma da fim ɗaya a fim ɗin ɗaya, wato Juyin Sarauta’.

Ko a watan Nuwambar da ya gabata (2020), Malam Gidan Dabino (MON) ya samu nasarar lashe kyautar Jarumin Jarumai a gasar mawaƙa da fina-finai ta Afrika ta Yamma, wato West African Music and Movie Awards (WAMMA Awards) da aka gudanar a Yamai, babban birnin Ƙasar Nijar, da fim ɗin Kwana Casain, a vangaren diramar talbijin mai dogon zango, inda ya lashe kyautar Jarumin Jarumai (Best Actor in a TV Series).
Kafin mu kai mai karatu ga tattaunawar tamu, bari mu yi waiwaye, don tuna wa mai karatu wane ne Ado Ahmad Gidan dabino (MON)?

Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Arewacin Nijeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni, sannan ɗan wasa ne a shirin fina-finan Hausa kuma ɗan jarida. An haife shi a shekara ta 1964 a garin Ɗanbagina da ke qaramar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano. Ya girma a Unguwar Zangon Barebari a cikin Birnin Kano. Ya fara karatun allo a makarantar Marigayi Malam Rabiu a Unguwar Zangon Barebari a shekarar 1968. Ya ci gaba da karatun littattafai na islamiyya a makarantar Marigayi Sheikh Tijjani Na ’Yanmota (1971).

Bai samu damar yin karatun boko yana ƙarami ba, sai da ya girma sannan ya shiga makarantar ilmin manya ta Masallaci ‘Adult Evening Classes’ Kano, a shekara ta 1984 zuwa 1986. Ya yi makarantar sakandare ta dare G.S.S. Warure Evening Session’ Kano, a shekara ta 1987 zuwa 1990. Ya shiga Jami’ar Bayero inda ya samu takardar shaidar Diflomar ƙwarewa a kan yaɗa labarai, wato ‘Professional Diploma in Mass Communication’ a Sashen Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005.

Ya rubuta littattafai da aka buga su kamar haka: ‘In Da So Da ƙauna’ 1-2. ‘Masoyan Zamani’ 1-2, ‘Hattara Dai Masoya’ 1-2, ‘Wani Hani Ga Allah’ 1-2, ‘Duniya Sai Sannu’ da ‘Kaico!’, ‘Malam Zalimu’ (wasan kwaikwayo) da ‘Malam Zailani’ ci gaban Malam Zalimu (wasan kwaikwayo) ‘Ina Mafita’ (wasan kwaikwayo) da ‘Daƙiƙa Talatin’ (wasan kwaikwayo) da ‘Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita?’ da ‘Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Muktar Adnan’ (tarihi), wanda suka rubuta tare da Sani Yusuf Ayagi da ‘From Oral Literature to Video: ‘The Case of Hausa’. (Takardun da suka gabatar a jami’a Hamburg, Jamus, shi da Farfesa Abdalla Uba Adamu).

An kuma fassara wasu daga cikin littattafansa guda uku daga harshen Hausa zuwa Turanci: ‘The Soul of My Heart’ (Fassarar In Da So Da ƙauna) da ‘Nemesis’ (Fassarar Masoyan Zamani) da kuma Kaico! (Fassarar Kaico!) ‘Young Women Substance Abuse and The Way Out’ (Fassarar Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita?)

Ya gabatar da muƙalu da dama a tarurrukan ƙara wa juna sani a cikin Nijeriya da ƙasashen waje. Wasu daga cikin takardun nasa an buga su a cikin kundaye (littattafai). Yana yin rubuce-rubuce a cikin jaridu da mujjalun Hausa. Tare da shi aka kafa wasu ƙungiyoyi, kamar ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen Jihar Kano, (ANA) a shekara ta 1992, kuma ya riqe shugabancinta na tsawon shekara uku da ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Jihar Kano, (Kano State Filmmakers Association) wanda a halin yanzu shi ne shugaban riqo na ƙungiyar Marubuta ta Raina Kama (Raina Kama Writers Association) wanda kuma shi ne shugabanta. Ya tava gabatar da shirin ‘Alƙalami Ya Fi Takobi’, a gidan rediyo Freedom Kano da kuma shirin ‘Duniyar Masoya’ a gidan rediyo Shukura FM da ke Damagaram, Ƙasar Nijar.

Harkar rubuce-rubuce da kuma wallafa ta ba shi damar zuwa ƙasashe fiye da goma sha biyar na Afrika, sannan kuma a ƙasashen Turai ya samu zuwa London da France da Italy da Holland da kuma Germany. Ya zama zakaran gasar rubutun wasan kwaikwayo ta shekarar 2009 ta tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir Ƙaraye, a Abuja, Nijeriya. Ya samu takardun yabo da dama daga jami’o’i da ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da gwamnati, saboda gudummawa iri-iri da yake bayarwa waɗanda suka shafi harshen Hausa da adabi da al’adu ta fannin rubuce-rubuce da shirin fina-finai da aikin jarida da harkokin ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da kuma gwamnati. 

A ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 ya sami takardar yabo daga Inuwar Jama’ar Kano, (Kano Forum) cikin mutane goma sha ɗaya da aka yaba da su a Jihar Kano wajen bayar da gudummawa game da ci gaban al’umma. Sannan a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta qasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama’a da yake yi a cikin ayyukansa. A shekarar 2017 ya samu zuwa matsayin tantancewa ta ƙarshe (nomination) a gasar fina-finai ta Zuma Film Festival da ke Abuja a matsayin jarumin jarumai na Afrika. A shekarar 2018 ya samu nasarar lashe kambun jarumin jarumai har sau uku a cikin gasar AMMA Award da ‘Kaduna International Film Festival’ da ‘Arewa Entertainment’, sannan ya amshi kambin mai shirya fina-finai da ya zarce kowane (Best Producer) a KILAF Film Festival duk a cikin fim ɗin ‘Juyin Sarauta’. A shekarar 2019, ya sake zama jarumin jarumai (Best Actor in Leading Rule) sannan ya amshi kyautar alƙalan gasa (Golden Jury Award) a gasar Kaduna International Film Festival.

Yana cikin wasu ƙungiyoyi kamar haka: ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’, (MOPPAN) da ‘Association for Promoting Nigerian Languages and Culture’, (APNILAC) da ‘West African Research Association’ (WARA) da ‘Indigenous Languages Writers Association of Nigeria’ (ILWAN) da sauransu.Mutum ne mai sha’awar tafiye-tafiye da rubuce-rubuce da bincike-bincike. Yana da mata ɗaya da yaya biyar. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ne Shugaba kuma Daraktan Gudanarwa na kamfanin Gidan Dabino International Nigeria Limited.

Da ɗan wannan bayani kan rayuwar fasihin gwarzon, za a iya fahimtar wasu daga cikin dalilan da suka sanya jarumin ya ke mamaye sha’anin kyautar kambun Jarumin Jarumai. To, amma a mako mai zuwa za mu kawo muku cikakkiyar tattaunawar Manhaja da wannan zaƙaƙurin fasishi a makon gobe da yardar Allah, domin ya warware mana zare da abawa kan sirrin waxannan nasarorin.