An Gudanar da kwas ɗin horar da ƙwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a Ƙasar Zimbabwe

Daga CMG HAUSA

An gudanar da bikin ƙaddamar da kwas din horar da ƙwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a cibiyar masu kula da alluran dake birnin Harare na ƙasar Zimbabwe, inda likitoci da masu ba da jinya daga wurare daban daban na ƙasar Zimbabwe 20 suka halarci kwas din na tsawon watanni 3, da koyon fasahohin ba da jinya ta alluran gargajiya na Sin, ta yadda za su yayata fasahohin zuwa wurare daban daban na ƙasar Zimbabwe don amfanawa jama’ar ƙasar.

Shugaban kula da kwas din kuma shugaban tawagar likitocin Sin dake kasar Zimbabwe Zhu Wei, yana fatan kwas din zai taimakawa ƙasar Zimbabwe wajen horar da ƙwararru a wannan fanni, kamar kafa wata tawagar ƙwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin a ƙasar, wadda za ta iya samar da hidima ga jama’ar ƙasar.

Sakataren ma’aikatar harkokin kiwon lafiya ta ƙasar Zimbabwe Jasper Chimedza ya bayyana cewa, fasahar jinya ta gargajiya ta ƙasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ba da jinya kan matsalar da ta shafi ciwon jiki, da numfashi da sauransu, kwas din zai horar da ƙwararru a wannan fanni, kuma hakan zai amfanawa jama’ar ƙasar.

Fassarwar: Zainab