Ƙasar Sin ta yi kira da a warware savanin siyasa a yammacin Afirka da Sahel ta hanyar shawarwari

Daga CMG HAUSA

Mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Dai Bing, yi kira da a gudanar da tattaunawa domin warware sabanin siyasa da ake fama da shi a yammacin Afirka da yankin Sahel.

Da yake jawabi a yayin zaman kwamitin sulhu na MƊD game da ofishin MDD mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS) a ranar Alhamis din da ta gabata, Dai Bing, ya ce tilas ne a ƙara kaimi “don tsayawa tsayin daka kan turba madaidaiciya wajen warware bambance-bambancen siyasa a yammacin Afirka da Sahel ta hanyar tattaunawa.”

Da yake karin haske kan zabuka a ƙasashen Najeriya da Senegal da Saliyo da Benin da Togo da dai sauransu kuwa, Dai ya ce, ya kamata ƙasashen duniya su mutunta ‘yancin kai da shugabancin ƙasashen yankin, su kuma ba su goyon baya wajen bin hanyoyin ci gaba da suka dace da yanayin kasashensu, tare da tallafawa bangarorin da abin ya shafa, wajen warware sabanin ra’ayi ta hanyar tattaunawa.

A baya-bayan nan ne dai, ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka wato ECOWAS, ta gudanar da taron koli, inda ta yanke wasu muhimman shawarwari kamar dage takunkuman da aka sanyawa ƙasar Mali.

Jakadan ƙasar Sin ya bayyana cewa, ƙasar Sin tana goyon bayan Afirka wajen lalubo hanyoyin warware matsalolinsu da kansu, kana tana goyon bayan ƙungiyar ECOWAS, wajen ci gaba da yin shawarwari da ƙasashen da ke fuskantar sauyin siyasa, tare da ciyar da harkokin siyasa gaba ta hanyar da ta dace.

Mai fassara: Ibrahim