Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Sin ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Ƙasar Amurka a Indinusiya

Daga CMG HAUSA

Yau ne, ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken a gefen taron ministocin harkokin wajen ƙasashen G20 a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia.

Wang ya bayyana cewa, a halin yanzu, dangantakar da ke tsakanin ƙasashen Sin da Amurka na cikin wani mawuyacin hali, wanda gwamnatin Amurka da ta shude ta haddasa, har ma tana kara fuskantar ƙalubale. Babban dalili kuma shi ne, kasar Amurka tana da matsala game da yadda take kallon ƙasar Sin, kuma manufofinta game da ƙasar Sin sun kauce daga hanyar da ta dace.

Wang Yi ya jaddada cewa, tun da ƙasar Amurka ta yi alƙawarin ba za ta nemi sauya tsarin ƙasar Sin ba, ya kamata ta mutunta tsarin gurguzu mai sigar musamman ta ƙasar Sin da jama’ar ƙasar Sin suka zaɓa, kana ta daina neman bata suna da taƙalar tsarin siyasa da manufofin cikin gida da waje na ƙasar Sin.

Tun da Amurka ta yi alƙawarin cewa, ba za ta nemi tayar da wani “sabon yakin cacar baka ba”, to, ya kamata ta yi watsi da wannan tunani kwata-kwata. Tun da Amurka ta yi alƙawarin ba za ta goyi bayan ‘yancin kai na yankin Taiwan ba, ya kamata ta daina neman yin illa da jirkita manufar Sin daya tak a duniya, da kuma daina fakewa da batun yankin Taiwan domin kawo cikas ga shirin sake dinkuwar ƙasar Sin cikin lumana.

Tun da Amurka ta yi alkawarin cewa, ba ta da niyar tayar da wani rikici da ƙasar Sin, kamata ya yi ta mutunta iko da cikakkun yankunan ƙasar Sin, ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma kaucewa cin mutuncin halastacciyar moriyar ƙasar Sin ta hanyar fakewa da batun kare haƙƙin dan Adam da tsarin demokuraɗiyya.

Blinken ya gabatar da manufofin Amurka game da ƙasar Sin, yana mai cewa, Amurka ba ta neman tayar da wani sabon yaki cacar baka kan ƙasar Sin, ko sauya tsarin ƙasar Sin, da ƙalubalantar matsayin JKS, da yi wa kasar Sin kawanya, ko kuma goyon bayan ‘yancin kai na yankin Taiwan. Amurka ta ƙuduri aniyar daidaita al’amurran da za su iya kawo cikas ga dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu, kuma tana son yin hadin gwiwa tare da ƙasar Sin ba tare da wata rufa-rufa ba.

Fassarawar Ibrahim