An gudanar da taron ƙaddamar da fim ɗin ‘Lu’u-Lu’u’

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Bayan kammala shirya katafaren fim ɗin wanda ya zo da wani sabon salo na ban mamaki. Kamfanin shirya finafinai na ‘Kannywwod Executive’ ya shirya taron ƙaddamar da shi kafin a ɗora shi a shafin su na ‘YouTube’ wanda a ke sa ran za a fara kallon sa a farkon shekarar nan ta 2022.

Taron, wanda aka gudanar da shi a ranar Litinin, 27/12/2021, a wajen taro na Ali Jita da ke Lawan Dambazau Road a Kano, ya samu halartar manya daga ciki da kuma wajen masana’antar finafinai ta Kannywwod.

Tun da farko da ya ke jawabi a wajen taron, furodusan fim ɗin na ‘Lu’u-Lu’u’, Isah Bawa Doro, ya bayyana cewa, “Mun shirya wannan taron ne domin mu tara mutane masu hikima da basira da kuma dattawa da masu ilimi a ɓangarori daban-daban, domin su kalli fim ɗin, su ba mu shawarwarin da suka kamata, tun kafin mu sake shi ga jama’a, domin komai na rayuwa da a ke son ya inganta, sai an samu shawara daga masana, to don haka ne muka shirya wannan taron, kuma alhamdu lillahi, kamar yadda kowa yake gani, mutane sun halarta, wanda hakan yake nuni da nasarar da ta ke cikin wannan aiki na mu. “

Dangane da abubuwan da fim ɗin ya ƙunsa kuwa, cewa ya yi, “mun yi ƙoƙrin fito da wata sana’a da ta ke ƙunshe da matsaloli kuma a yanzu kusan za a iya cewar babu wata sana’a bayan ta fim da ta fi ta ɗaukar matasa masu yawa, wato sana’ar jari-bola.

To mun yi duba da irin arziƙ in da yake cikin harkar, da kuma matsalolin da suke cikin ta, don mu wayar wa da mutane kai su gane ba kowa da yake cikin ta ba ne yake mutumin banza ba, harka ce da ta ke da rufin asiri da kuma samar da aikin yi ga matasa.”

Ya ƙara da cewar, “ganin yadda matasa suke zama kara zube babu aiki babu sana’a, don haka akwai buƙatar a haska mu su wasu sana’a’o’in da za su yi su riƙe kan su, duba da yadda rayuwa ta ke tafiya a yanzu, don gudun faɗawa munanan hanyoyi da suke ta ɓullowa a wannan lokacin.”

Furodusan Lu’u-lu’u, Isah Bawa Doro tare da Darakta Aminu Saira a wajen taron ƙaddamarwar da dim ɗin

Ya ci gaba da cewar, “A wannan lokaci, mu matasa ya kamata mu tashi mu samar wa kan mu aiki, mu bar dogaro da gwamnati, don haka mu riƙe ƙananan sana’a’o’i don mu zama masu dogaro da kan mu, kada mu jira cewar sai gwamnati ta samar mana da aiki. Kuma a wannan ɓangare kaɗai za mu tsaya ba, za mu ci gaba da taɓo wasu sana’a’o’in. Don haka a matsayin mu na matasa mu bar raina sana’a duk ƙanƙantar ta, domin komai da ƙarami yake farawa.

Don haka wannan fim ɗin ba kamar wanda aka saba gani masu ɗauke da rawa da waƙa ba ne, fim ne na kowa da kowa, wanda za mu ɗora shi a shafin mu na YouTube Kannywwod Exclusive. Ina fatan masu kallo za su bibiya domin ganin irin saƙon da fim ɗin yake ɗauke da shi.”

Taron dai ya samu halartar manyan Jarumai da mawaƙa da suka haɗa da Alhassan Kwalle, Sadik Sani Sadik, Ali Gumzak, Hassan Giggis, Sunusi Anu, Dauda Rarara, Aisha Humaira da sauran su.