Majalisar Dattawan Kannywood ta kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Bashir Tofa

Daga NASIR S. GWANGWAZO

A yammacin ranar Litinin, 3 ga Janairu, 2022, wato ranar da aka yi jana’izar marubuci kuma ɗan siyasa a Nijeriya, Alhaji Bashir Othman Tofa, rasuwa, Majalisar Dattawan Kannywood ta kai ziyarar ta’aziyya gidansa da ke Gandun Albasa a Birnin Kano.

Wannan ya biyo bayan taron da majalisar ta gabatar ne a daren Lahadin da ta gabata, wato 02 Janairu, 2022, inda ta shirya liyafar taya murnar shigowar sabuwar shekara lafiya, to amma sai aka wayi gari da rasuwar hamshaƙin dattijon ƙasar, inda nan da nan dattawan na Kannywood suka sake tattara kansu, suka ɗunguma wajen ta’aziyya. 

Sun kai ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawan, Alhaji Auwalu Isma’il Marshal, da Shugaban Gidauniyar Kannywood, Alhaji Shu’aibu Yawale, waɗanda suka yi addu’ar Allah ya ji ƙan mamacin tare da bayyana irin gudunmawar da ya ke bai wa harkar adabi, musamman a Arewa. 

An yi taron liyafar ne a babban ɗakin taro na Kannywood TV, inda kuma ya sami halartar dattawan masana’antar masu yawa, ciki har da mambobi da shugabannin majalisar da kuma wasu dattawa da suka yi fice a zamanin wasan kwaikwayo na gidajen talabijin na NTA Kano da CTV (ARTV) irin su Alhaji Garba Ilu Ɗankurma da Alhaji Bashir Ɗanmagori da Malam Isa Bello Ja da sauransu.

Taron liyafar, wanda aka yi jawabai masu ratsa jiki a yayin gudanar da shi, ya kalli matsalolin wannan masana’anta ta Kannywood da kuma yadda za a warware su dan samun cigaba. 

Wannan liyafa mai ɗimbin tarihi ta sami halartar manyan mutane irinsu futaccen jarumi kuma babban furodusa, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama, da furodusa kuma mamallakin gidan talabijin na Kannywood TV, Dr. Ahmad Sarari, da tsohon Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Fim ta Nijeriya Reshen Jihar Kano, Alhaji Kabiru Maikaba, da fitaccen jarumi kuma Mai Unguwar Mandwarai, Alhaji Ibrahim Muhammad Mandawari da sauransu. 

Bugu da ƙari, akwai fitaccen darakta kuma ƙwararren marubuci, Malam Bala Anas Babinlata, da ƙwararren marubuci kuma furodusa, Malam Khalid Musa. Haka nan akwai dattawa irinsu Jarumi Abdulahi Zakari (Ligidi) da jarumi kuma furodusa, Malam Adamu Muhammad (Kwabon Masoyi). Sannan kuma akwai irinsu Furodusa Gwanja, Muhammad Gumel, Yakubu Liman, Yakubu Ibrahim Yakasai da sauransu.