Talla jami’a ce ta lalacewar ‘ya’ya mata – Dakta Fatsuma Dada

“Ni ce Muƙaddashiyar Magatakarda ta farko a jami’ar Yobe”

Daga ABUBAKAR A. BOLARI

Dakta Fatsuma Dada Muhammad, ƙwararriyar Malamar jami’a ce da ta shahara a fagen koyarwa, har sunanta ya ɗaukaka ta kai matsayin sakatariya kuma muƙaddashiyar magatakardar jami’a mallakar Jihar Yobe YBSU ta farko. A zantawar ta da shafin Gimbiya na jaridar Manhaja, ta bayyana tarihin rayuwar ta da irin gwagwarmayar da ta sha a wasu ɓangarori. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.
DAKTA FATSUMA: Sunana Dakta Fatsuma Dada Mohammed. Ni ‘yar asalin garin Potiskum ce, a Jihar Yobe, kuma ‘yar ƙabilar Bolewa, a nan aka haifeni, na girma, aka sani makarantar firamare ta Kara (Kara Primary School Potiskum). Da na kammala na yi nasarar shiga Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta ‘Yan mata da ke garin Owerri (Federal Goverment Girls College Owerri) a wurin da na kammala jarrabawar WAEC na samu Sarifiket ‘Certificate’, Ina gamawa kuma na samu shiga jami’ar Bayero ta Kano wato ‘Bayero University Kano, a nan na samu digiri ɗina na farko a B.A Education a shekarar 1984. Sai na tafi hidimar ƙasa NYSC a Jihar Binuwai. Na gama a shekarar 1985, daga bisani na sake komawa jami’ar Maiduguri, na yi digiri na biyu wato ‘Masters degree’ nan ma a Education wato ɓangaren mulki da tsare-tsare wato ‘Administration and Planning’ a shekarar 1992, sannan na yi (Phd) wato ‘philosophy degree’ digiri na uku kenan a ‘Educational’ har ila yau a ɓangaren mulki da tsare-tsare ‘Administration and planning’ a jami’ar Bakht Al Ruda ta Ƙasar Sudan.
 
Bayan kammala karatu, kin fara aiki ne?
Bayan kammala NYSC ɗina an ɗauke ni aikin koyarwa, aka tura ni sakandaren Al’umma da ke garin Biu a Jihar Borno, wato ‘Community Secondary School’ Biu, don a lokacin ba a ƙirƙiro da Jihar Yobe ba, domin lokacin Yobe ɗin na ƙarƙashin jihar ta Borno ce, daga nan na zagaya makarantun sakandare da dama a matsayin malamar darasin Turanci wato ‘English Language’, da aka ƙirƙiro da Jihar Yobe, sai aka tura ni na zama shugabar makarantar sakandare wato ‘Principla’ ta GGSS Nguru a shekarar 1992. Na zagaya makarantu da yawa a matsayin ‘Principal’, kamar GGSS Ngelzarma da GGSTC Potiskum da sauran su. Na samu shekaru 14 ina matsayin shugabar makarantar sakandare, har zuwa shekarar 2006, daga nan likkafa ta ci gaba, aka mayar da ni hedikwatar Ma’aikatar Ilimi da ke garin Damaturu, ‘Ministry of Education Headquarters’ kenan, a Damaturu, a matsayin muƙaddashiyar darakta mai kula da harkokin makarantu,wato ‘Deputy Director School Services’, daga nan aka ƙirƙiro da jami’a mallakar Jihar Yobe, Yobe ‘State University’ wacce da farko ake kiran ta Bukar Abba Ibrahim ‘University’, kafin a canja mata suna, aka ɗauke ni aiki a wajen, a matsayin Babbar Mataimakiyar Magatakarda wato ‘Principal Assistant Registrar’. A shekarar 2008 aka ƙara min girma wato ‘Promotion’, zuwa Muƙaddashiyar Magatakarda wato ‘Deputy Registrar’, inda na zama ni ce Muƙaddashiyar Magatakarda ta farko a jami’ar.

Ko akwai ƙalubalen da kika fuskanta?
Da yake yawancin aikin da na yi a matsayin shugabar makarantar ‘yan Mata zalla ce, kuma ta kwana na yi, ma’ana (boarding schools) wanda muna tare da yaran ne sa’oi 24 a kullim wato ’24hrs a day’. Kiwon yara ba abu ne mai sauƙi ba, kuma a wannan matsayin ba wai ilimi kawai mu ke ba su ba, har da tarbiyyar su mu ke kula da ita da tsabtar su da kuma ci da shan su, ga kuma tafiyar da harkokin malamai da sauran su. To aiki ne mai cike da ƙalubale sosai, don kullun kawai ana kan aiki ne, amma duk da haka gaskiya alhamdu lillahi, na gama lafiya.

Na san ba a rasa nasarori ba. 
A duk tsawon shekarun da na yi ina aikin, makarantu ba a taɓa min wani bore ba, kuma ba wani mutuwan yara ko wani haɗari, na samu haɗin kan ɗalibai da ma’aikata na har ma ina da takardar yabo wato ‘Commendation letters’ guda 3 daga Ma’aikatar Ilimi wato ‘Ministry of Education’, kuma har yanzu akwai ƙauna da zumunci mai yawa daga tsofin ɗalibai da ma’aikata na. Har yau ina cin moriyar mu’amalar mu.

Rai aka ce da buri. Mene ne naki buri a rayuwa?
Burina a rayuwa shine, na yaɗa ilimi na kawar da jahilci, don ilimi shi ne ya bambanta mutum da dabba, kuma gishiri ne na zaman duniya.

Ina ki ke zuwa idan kin samu hutu?
Duk hutu na baya wuce cikin Jihar Yobe, tsakanin Damaturu da Potiskum. Ba na zuwa ko’ina dan yin hutu.

Iyali fa?
Allah ya albarkace ni da yara shida, kuma a yanzu biyar suna raye, huɗu maza, ɗaya mace, kuma ina tare da babansu, sannan Ina kuma da ‘ya’yan ‘yan’uwa wato ‘extended family’ wanda kamar ni na haife su.

Ƙasashe nawa ki ka ziyarta?
Na je Saudi Arabia aikin Hajj, kuma na je Indiya ‘international conference’, taro na ƙasa da ƙasa, na je Jamhuriyyar Benin ta hanyar aiki, kuma na je Sudan karatun Phd.

Dakta Fatsuma a bakin aiki

Ko Dakta na cikin wasu ƙungiyoyi?
Ni ce shugabar ƙungiyar cigaban mata, wato ‘President Native Women Advancement’, inda mu ke tallafa wa mata da marayu, Ina ‘Project officer’ a INOL Watau ‘Initiative for the needy, orphans, less previledge and widows’, kuma’ Research coordinator’ ta NCWS, ina ‘member’ a OGP, ‘Open Govt Partnership’ ta Yobe da sauran su. Waɗannan duka ‘voluntary organisation’ ne, ƙungiyoyin sa kai dan cigaban al’umma da kuma jin tausayi na ƙasa da mu.

Wane tufafi ki ka fi so?
Na fi amfani da atamfofi na mu na Ƙasar Hausa, don laushi da sauqin sarrafawa, domin ƙasarmu akwai zafi.

Mu koma ɓangaren abinci. Wanne ki ka fi so?
Na fi son tuwon laushi da miyar kuka, ko agushi ko ogbono.

Wacce shawara za ki ba wa mata ‘yan’uwanki?
Gaskiya mata su yi ƙoƙarin samun ilimi na zamani da na addini. Ilimi shi yake sa komai na rayuwa ya zo da sauƙi. Jahilci cuta ce babba. Don haka, na ke bai wa iyaye shawara, su mayar da hankali kan karatun ‘ya’ya mata. Kar a fifita kararun namiji akan mace, sannan iyaye su sani, talla da ake ɗaura wa ‘ya’ya mata bai dace ba, domin talla jami’a ce ta lalacewar ‘ya’ya mata. 

Madalla, mun gode.
Ni ma na gode.