
Daga BELLO A. BABAJI
Wani ɗan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal mai suna John Ssenyonga ya rasa ransa bayan harbe shi da aka yi a daren ranar Laraba, a lokacin da ya ke murnar doke Manchester United da ci 2 da nema da ƙungiyar ta yi.
Lamarin ya auku ne a wani gidan cin abinci dake garin Lukaya, kilomita 100 tsakanin sa da babban birnin ƙasar, Kampala.
Haka ma wani daga cikin magoya bayan ya samu rauni a lokacin da maharbin ya buɗe wuta wa jama’a ana tsaka da kallon wasan.
BBC ta ruwaito cewa manajan gidan ya fusata ne sakamakon surutai da suka yawaita wanda hakan ya sa ya umarci ɗaya daga cikin masu gadi da ya yi ƙoƙarin taiƙata ɗaga murya da ake yi.
Daga nan ya gargaɗi masu kallon da su rage surutu inda suka cigaba ba tare da ƙauƙautawa ba wanda har ta kai ga manajan ya kashe wutar lantarkin gidan baki ɗaya.
Jami’an ƴan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin tare da alla-wadai da faruwarsa, kamar yadda kakakinsu, Twaha Kasirye ya bayyana.
Wannan shi ne karo na biyu da irin hakan ya ke faruwa a ƙasar cikin wata uku inda a Oktoba ne aka kashe wani ɗan Manchester United mai suna Benjamin Okello a Kyobugombe, lokacin da Arsenal ta yi 2 da 2 da Liverpool.
