Abubuwan da yarjejeniyar Nijeriya da Faransa ta ƙunsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A makon nan ne aka ƙulla yarjejeniya tsakanin Nijeriya da Faransa don samar da ayyukan haɗin-gwiwa da za su inganta harkokin ma’adanai a ƙasashen biyu.

Ma’adanan sun haɗa da jan ƙarfe (Copper), Lithium, Nickel, da Cobalt.

A cikin yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka rattaɓa hannu yayin ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙasar ta Faransa, sun amince da yin haɗin-gwiwa kan bincike da horar da ɗaliban ƙasashen biyu domin musayar ilimi da samar da ƙwarewa.

Babban abin da ke cikin yarjejeniyar shine haɓaka ayyukan haƙar ma’adinai masu ɗorewa ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da za su rage gurɓatar muhalli da ruwa yayin haƙar ma’adinai.

Ministan ci-gaban ma’adanai na Nijeriya, Dakta Dele Alake ne ya rattaɓa hannu akan yarjejeniyar a madadin Nijeriya, yayin da wakilin Ma’aikatar Kula da Ma’adanai da Ƙarafa na Faransa, Benjamin Gallezot, ya sanya hannu a madadin Faransa.

Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta buɗe sabbin damammaki na gyaran ramuka sama da 2,000 da aka yi watsi da su a cikin ƙasar ta hanyar shirinta na ayyukan gyara muhalli da haƙar ma’adanai.

Yarjejeniyar tana daga ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na inganta ɓangaren haƙar ma’adanan domin yin kafaɗa-kafaɗa da takwarorinmu na duniya.

By Babaji