‘Yar Ibori da wasu ƴan Majalisar Wakilai na LP biyar sun koma APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mambobin jam’iyyar LP a Majalisar Wakilai guda biyar ne suka sauya sheƙa zuwa jami’yya mai mulki ta APC.

Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a zauren Majalisar.

Ƴan majalisar sune; Chinedu Okere da ke wakiltar mazaɓar Owerri Municipal/Owerri ta Arewa/Owerri ta Kudu; da Mathew Donatus, mazaɓar Ƙaura a Kaduna; da Akiba Bassey, Calabar Municipal/Odukpani; da Esosa Iyawe, Oredo; da kuma Hon. Fom Dalyop Chollom (Barkin Ladi/Riyom).

Haka ma Erhiatake Ibori-Suenu wadda ƴar majalisar ce daga Delta kuma ƴar tsohon gwamnan jihar James Ibori ta fice daga jam’iyyar PDP inda ta koma APC.

A lokacin da ya ke magana game da sauya sheƙar, ɗan majalisa Matthew (Ƙaura-Kaduna) ya ce sun yi hukuncin ne bisa zaɓinsu.

By Babaji