An kafa dokar hana fita a Kano

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa dokar hana zirga-zirga a jihar bayan da INEC ta ayyana wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar.

Kwamishinan Labarai na jihar, Mohammed Garba ne ya ba da sanarwar hakan da safiyar nan.

Ya ce, an kama dokar ce gudun kada wani rikici ya ɓarke a jihar bayan sanar da wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da INEC ta yi.

Manhaja ta rawaito yadda yara ƙanana, matasa da sauransu suka mamaye wasu titunan Kano saboda murnar nasarar da Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu na zama gwamna mai jiran gado a jihar.

Da ma dai Rundunar ‘Yan Sandan jihar, ta haramta wa jama’a yin dafifi da zagaye a titinan jihar da sunan murnar lashe zaɓe.