An kama mai shekara 40 da ya yi wa ‘yar shekara uku fyaɗe har ta mutu a Kano

Fyade

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an tsaro sun kama wani dattijo mai shekara 40 da ake kira Baba Idi sakamakon zargin da ake yi masa na yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekara uku fyaɗe, abin da ya yi sanadin rasuwarta a Kano.

Kamar yadda wani ɗan’uwan marigayiyar ya bayyana, Yasmin ta rasu ne ranar Alhamis 29/09/2022 da ƙarfe 4 na yamma a dalilin fyaɗen da aka yi mata ranar Talata.

Wanda ake zargin ya yi fyaɗen, Baba Idi, yana zaune ne a Lungun Alhaji Halliru a unguwar Gama, Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Baba Idi ya ɗauki Yasmin ya kai ta ɗakinsa ya ba ta alewa, inda ya yi lalata da ita, kuma ya tsoratar da ita cewa in dai ta faɗa wa Abbanta sai ya kashe ta da almakashi, kuma zai haɗa ta da magen gidansu ta cinye ta.

Makusantan Yasmin sun tabbatar da cewa ta kwatanta masu yadda ya ɗora mata almakashi a wuya ya ce sai ya yanka ta da shi idan ta faɗa wa Abbanta.

Bayan ta shigo gida an cire mata kaya za a yi mata wanka aka ga jini yana fitowa daga gabanta. Aka ce me ya same ta? Ta ce, “Baba Idi ne yake mun wani abu yau ma ya cire min wando ya yi min, ya ba ni alawa, kuma ya ce idan na faɗa wa Abbana zai kashe ni. Umma don Allah kar ki faɗa wa Abba.”

Daga nan aka ɗauke ta aka kai ta asibiti, inda likitoci suka tabbatar da an shige ta, kuma suka faɗi hanyoyin da za a bi a kula da lafiyarta.

Bayan jami’an tsaro sun kama Baba Idi sun kai shi ofishinsu, inda ya rubuta bayaninsa. Ana fito da shi da ankwa, Yasmin tana ganin sa ta ruɗe da firgici tana cewa “Umma ya ce kashe ni zai yi da almakashi! Me ya sa kika faɗa wa Abba? Kashe ni zai yi, kuma zai haɗa ni da mage.”

Daga nan zazzaɓi ya kama ta aka dawo da ita gida, har zuwa washegari da ta rasu tana ta maimaita “kashe ni zai yi da almakashi.”

Har ya zuwa haɗa wannan rahoton, rundunar ‘yan sanda ba su ce komai a kan lamarin ba.