Nnamdi Kanu ya rubuta wa Buhari wasiƙa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jagoran Ƙungiyar ‘Yan a-ware ta IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, ya aika takardar ƙorafi ga Shugaba Muhammadu Buhari inda ya nemi gwamnati ta sake shi cikin gaggawa.

Gwamnatin Nijeriya na tuhumarsa da laifuka guda 11, ciki har da cin amanar ƙasa da ta’addanci, da mallakar haramtattun makamai, da kuma ƙoƙarin tunzura jama’a don haifar da yamutsi.

A cikin wasiƙar wadda rukunin lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Mike Ozekhome mai lambar SAN suka fitar, Nnamdi Kanu ya buƙaci Shugaba Buhari ya bada umarnin sakin sa daga hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS don bin wata hanyar cimma masalahar siyasa.

Wasiƙar ta ce: “Kana iya yin hakan ta hanyar umartar ministan shari’a na tarayya don ya yi amfani da ikonsa a ƙarƙashin sashe na 174 na tsarin mulkin 1999 ya shigar da ƙudurin ‘babu muradin gurfanarwa a kotu wato (nolle prosequi)’.

“Hakan zai kawo qarshen zaman ɗar-ɗar ɗin da ake fama da shi da kuma umarnin zaman gida da a yanzu suka addabi yankin Kudu maso Gabas kuma ya kassara harkokin kasuwanci da rayuwa kamar yadda aka saba”, inji takardar ta Nnamdi Kanu.

A shekarar 2021 ne gwamnatin Nijeriya ta ba da sanarwar sake kama Nnamdi Kanu, inda ta sake gurfanar da shi a gaban kotu.