Mutum 450 sun samu horon koyon sana’o’in hannu a cikin shirin Sanatan Kebbi ta Arewa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirinsa na yaƙi da zaman banza, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa ya horar da matasa maza da mata 450 sana’o’in hannu da suka haɗa da yadda a ke yin takalmi da bel da kuma alabai (wallet) a ƙananan hukumomin Argungu da Augie da kuma Arewa.

Da yake jawabi wajen bikin yaye waɗannan matasan a garin Argungu a madadin Sanata Dokta Yahaya, Alhaji Sama’ila Dantagago ya ce dalilan da suka sanya Sanata ɗaukar wannan matakin shi ne saboda rage zaman banza da dogara ga gwamnati wanda idan mutum yana da sana’a ba wata barazana da za ta tayar masa da hankali, “saboda haka yin riƙo ga sana’a shi ne mafi a’ala musamman a irin wannan lokacin da rayuwa ta yi tsada.”

Ya yi kira ga matasan da suka ci moriyar wannan shirin da su yi amfani da kuɗaɗen da aka ba su wajen sayen kayan aiki saboda su cigaba da aiwatar da sana’o’in hannu da suka koya.

Malama Amina Muhammed tana daga cikin waɗanda suka ci moriyar shirin ta yaba wa Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi bisa ga ƙoƙarin sa na tuna baya saboda bata tava jin wani ɗan siyasa yana yin haka ba saboda haka ta yi kira ga ‘yan siyasa da su yi koyi da shi.

Nasiru Abubakar yana daga cikin matasan da suka samu nasarar shiga cikin matasan da suka ci gajiyar shirin, shi ma ya bayyana cewa ya daɗe da kammala karatu amma ba wani aiki da ya ke yi amma yanzu ya ce zai tsaya tsayin daka don ya dogara ga kansa.

Ya nuna jin daɗinsa bisa ga irin kulawar da su ke samu daga Sanata Yahaya Mallamawan Kabi.

Ya ce an sha yin irin wannan a baya amma dai sai wannan karon ya samu shiga, saboda haka yana godiya tare da alƙawarin amfani da wannan ranar da ya samu.

Aikin koyon sana’o’in da aka gudanar ya ƙunshi ƙananan hukumomin mulki na Argungu da Augie da kuma Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *