Maulidi: Gwamnati ta ayyana Litinin mai zuwa ranar hutu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar hutun gamari domin bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) na bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan, inda ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar Musulmi na gida da waje murnar zagayowar wannan rana.

Rana 12 ga watan Rabi’ul Awwal al’ummar Musulmi kan yi bikin mauldi, wanda a bana ranar ta faɗa a Asabar wanda hakan ya sa gwamnatin ayyana Litinin mai zuwa ranar hutu.

Daga nan, Aregbesola ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan dama wajen koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW), yana mai cewa yin hakan zai taimaka wajen samun ingantaccen tsaro da zaman lumana.

A ƙarshe, Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman Musulmi, da su guji tada fitina, karya doka da duk wani nau’i na laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *