An kama ’yan Chana suna haƙar ma’adanai a Nasarawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta tarwatsa wani katafaren wurin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a garin Rafin Gabas da YA ke ƙaramar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa, inda suka cafke wasu ‘yan ƙasar Chana uku da suke gudanar da ayyukan haaar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Rundunar, ƙarƙashin jagorancin jami’an NSCDC na musamman kan ma’adinai, ta hanyar leƙen asiri ne da kuma haɗa kai sun kutsawa wurin, inda dakatar da ayyukan da ba su dace ba.

A cewar kwamandan ma’adinan na musamman, mataimakin kwamanda John Onoja Attah, rundunar ta yi nasarar kutsawa cikin haramtacciyar cibiyar haƙar ma’adanai duk da yunƙurin da wasu da ake zargin suka yi na tserewa daga jami’an tsaro.

“Wannan wani babban ci gaba ne a yaƙin da muke yi na kawar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, muna ci gaba da tarwatsawa tare da kame ɓaragurbin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, tare da tabbatar da cewa masu aikata laifuka sun fuskanci shari’a,” inji Attah.

Bayan kai farmakin, an kulle wurin da ake haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, kuma an fara farautar waɗanda suka tsare.

Attah ya kuma tabbatar da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin bankaɗo masu hannu a cikin wannan aika-aika, ciki har da duk jami’an tsaro da aka samu suna taimakawa wajen haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar NSCDC ta yi alƙawarin ci gaba da daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin ƙasar, tare da gargaɗin masu zagon ƙasa kan tattalin arziki da su daina ko kuma su fuskanci cikakken fushin doka.

By ukarofi