Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Akasarin lokatai, fushi sai ya sa mu manta da cikakkiyar koyarwar Manzo (SAW) da Qur’ani. kuma ba mu da shiryarwa da ta wuce su.
Idan muka tuna da labarin Ka’ab Bn Zuhayr (Ibn Kathir ya kawo labarinsa), wato wani mashahurin mawaƙin ƙuraishawa kuma ɗan gado, wanda ya yi ta sakin baituka na cin mutuncin Manzo (SAW). Wasu sahabbai su ka yi ta farautar sa. A ƙarshe ya yi ‘disguise’ (ɓadda-bami) ya je fadar Manzo (SAW) ya nemi gafara kai tsaye ga Annabi (SAW). Bayan bayyana kansa, su Sayyadina Umar (RA) suka zare takobi za su kashe shi, amma Annabi (SAW) ya hana su kuma ya karɓi tubansa.
Ka’ab Bn Zuhayr ya musulunta, sannan ya yi baituka na yabon Annabi (SAW), wanda suka faranta ran Manzo (SAW) har ya ɗauki wani gwado nasa ya ba shi kyauta. Har ya mutu ya na hidimta wa Musulunci. A bayan wafatin Manzo (SAW), Mu’awiyya Bn Abu Sufyan ya nemi Ibn Zuhayr ya fansar masa da gwadon a kan dirhami 10,000, amma ya ƙi. Sai bayan mutuwarsa magadansa su ka siyar wa Mu’awiyya (AS) gwadon a kan kuɗi dirhami 20,000. Tun zamanin Umayyads har zuwa Abbasids da Daular Ottomon wannan gwado ake ajiye da shi a matsayin tarihi. Yanzu haka ya na nan a ƙasar Turkiya a fadar Tockapi.
Kun ga Annabi (SAW) ya juyar da ƙiyayya zuwa ga soyayya, yadda gwadonsa ya fiye wa Ka’ab dukiya mai tarin yawa irin ta waccan lokaci. Akasari da irin wannan ɗabi’ar Annabi (SAW) ya mamaye mutane ba da zafi ko barazana ba.
Sannan idan ka koma Qur’ani, me Allah ya ce game da masu ɓatanci ga Manzo (SAW)?
Q33:57 “Lallai waɗanda ke cũtar Allah da Manzonsa Allah Yã la’ance su, a cikin dũniya da lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãqantarwa”
Duk wanda ya taɓa Manzo (SAW), Allah ya yi masa tanadi mai tsanani.
Don haka idan a wurinka maganar Marigayi Dr. Tanshi cewa ba ya buƙatar taimakon Manzo (SAW), ba ta dace ba, to fahimtarsa ce. Idan kai kuma ka yarda ka na neman taimakonsa, shi kenan sai ka ƙyale shi da fahimtarsa, ka rungumi taka. Tabbas a lahira kowa zai gane shin ko Manzo (SAW) na iya taimako ko a’a? Idan ya kasance zai yi taimako, to ka ga ana buƙatar taimakonsa, idan kuma ba zai yi taimako ba, ka ga ba a buƙatar taimakonsa kenan. Kuma dole dai cikin biyun a sami ɗaya, domin e da a’a ba sa taɓa zama a hurumi guda.
Don haka kowa dai ya riƙi hujja da zai kare kansa a waccan rana mai zuwa. Kuma shi ya sa Allah da kansa ya umarci Manzo ((SAW) ya ce da, hatta kafiran Makka “Lakum dinikum waliyadin” ballantana mu a tsakanin mu Musulmi, mu dage lallai fahimta ta dole kowa ya bi ta?
‘Please Let’s agree to disagree…the only way we could definitely be a much better’ Umma insha Allah.
Malam Ali marubuci ne kuma manazarci mazaunin Kano
