Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Kamar yadda ya rayu cikin ‘controɓersy’ sakamakon yadda ya fahimci addini, haka mutuwarsa ta zama da ‘controɓersy’ tsakanin masu ganinsa a kan daidai da waɗanda su ke ganin wabinsa. Duk wani ɗan adam, musamman wanda ya shahara a wani fage na rayuwa, kamar yadda ya ke da masoya da maƙiya haka idan ya mutu za ka ga wannan soyayya ko ƙiyayya ta dada bayyana, hatta annabawa.
A cikin al’adu da addinai na ɗan adam, kama daga Kiristanci, ’yan Buddha, ’yan Hindu, Musulmi kai hatta masu addinai na gargajiya za ka samu su na da wata doka cewa, kada a yi ɓatanci ga mamaci. Wannan ‘uniɓersal’ ɗabi’ar idan ka kalle ta da kyau, za ka gano wani babban darasi wanda shine hikimar yin hakan. Wato da zarar mutum ya mutu, duk wani zance da zai biyo baya a kansa, bai wuce fata ba. Ko dai masoya su yi fatan rahama a gare shi, fatan da ba shi da tasiri a kan mamacin a wajen Allah, matuƙar ya kasance wanda ƙarara ya yi adawa da samuwar Ubangiji ne, kamar yadda ya zo cikin
Q9:84 “Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lallaie ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai”
Wannan aya ta sauka a kan munafukai da ke amsa Musulunci, amma babu shi a zuciyarsu. Wato bayan Manzo (SAW) ya sallaci Ibn Salul, ya bayar da gwadonsa an yi masa likkafani kuma ya raka gawar kabari. Sai Allah ya saukar da wannan aya ta hanin aikata hakan ga Manzo (SAW).
Ko kuma a ɗaya ɓangaren, makiya da ke fatan azaba ga mamacin, wanda shi ma burinsu ba zai wanzu ba face dai abinda mamatan suka kasance sun aikata kamar yadda Allah ya sanar da mu cikin
Q2:141 “Waccan, wata al’umma ce, tã riga ta shige, su na da abin da suka sana’anta kuma kuna da abin da kuka sana’anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa”
Wato kun ga duk wani wanda ya mutu, ya fado karkashin wannan aya cewar ya riga ya shige kuma Allah na sane da abinda kowa ya aikata, walau mamacin ko wanda ke raye, ba wani cikinsu da zai iya canza sakamakon dayan domin kawai ya na fata ko na rahama ko na azaba ga mamacin. Wannan aya ta kewaye daya daga cikin manyan ikirari na Dr Idris da masu irin fahimtarsa na cewa iyayen Manzo Allah na wuta. Wannan hurumi ne na Allah kamar yadda wannan aya ta jaddada, ba wani Rai da ke da hurumin sanin tabbas wane Dan wuta ne.
Akwai maganganun Dr Idris da ke kafirta duk wani wanda baya bin da’awar salafiyya da kiransa mushriki. Da maganar ba ya neman taimakon Annabi. Har da zancen rashin ta’aziyar mamata Yan maulud da suka mutu a hadari da harin bom ya na cewa sun hallaka kansu a banza. Wadanda abubuwa ne da Allah kadai zai yanke masa hukunci bisa adalci ba wani ba. To, shi dai ya amsa kiran ubangijinsa kuma babu wanda zai hana magoya bayansa kyautata zaton rahama gare shi, ko kuma makiya su kyautata zaton azaba gare shi, amma duk biyun a zaton za su kasance, domin Allah kadai ya san hakika.
A karshe dai, kowa da ka sani, dole zai fuskanci tsayuwa gaban Allah kuma abinda Allah ya yi alkawari shine
Q21:47 “Kuma Munã aza ma’aunan ãdalci a Rãnar kiyãma, sabõda haka ba a zãluntar wani rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãyar zarra ne, sai Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi”
Wannan shine zai baiwa kowanne mu passport na shiga aljanna ko wuta sakamakon ayyukanmu. Kuma Allah shi ya fi kowa sanin dalilin mu da yanayin ayyukanmu, don haka shi kadai zai iya tantance mu sakamakon auna wadannan ayyuka namu.
Kamar yadda Facebook ke dauke da duk wani motsin da muka taba yi a cikinsa, haka marubuta ke nadar ayyukanmu. Don haka duk wani Mai hankali, kamata ya yi hakilon sa ya kasance na cewa “wane aiki na alheri na yi tsawon rayuwata ta?” Domin yawan wannan alheri shine zai sahale maka passport dinka na shiga aljanna, ba wani fata na wasu mutane ba, haka nan mugun fata ba zai taba kai ka wuta ba, face abinda ka sana’anta. Idan akwai wani abu da ya cancanci ya zame mana babban darasi, bai wuce mutuwa ba. Kamar yadda Dr Idris ya wuce, muna nan a bayansa ko yau ko gobe, kuma kowa ya yarda da haka, koda kuwa mutum bai yarda da samuwar Allah ba. Dole ya yarda da mutuwa, wato iya kadai ce reality da babu mai adawa ita.
Don haka ko ka yiwa Dr Tanshi fatan shiga aljanna, ko shiga wuta…iyakarsa kenan dai, fata. Hakikatan na wurin Allah, shi kadai ne masanin gaibu. Kuma a ranar wannan tantancewa, ba wani wanda zai je wajen yiwa Dr Tanshi hisabi a matsayin lauya mai kariya, ko shaida mai zugawa, domin kaima ta kanka ka ke yi.
Allah ka ji kan Dr Idris Tanshi ka kyauta namu zuwan.
Ali Sadiq ƙwararren manazarci ne a Kano
