An kama ‘ya’yan attajiri, Nasidi da tsabar Dala miliyan 6.1 a filin jirgin Legas

Spread the love

Jami’an tsaro a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas sun cafke wasu fasinjoji biyu (Mahmud Nasidi da Yahaya Nasidi) da ake zargin daga jirgin ‘Aero Contractors’ suke da tsabar kuɗi sama da Dala miliyan 6.1 a hannunsu.

Wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana a bainar jama’a, sun shaida wa manema cewa wasu samari ne da ake zargin suna da alaka da wani da aka fallasa siyasarsa ne ke safarar kuɗaɗen.

Duk da cewa har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto ba, majiyoyin sun ce jami’an Hukumar Tsaron Jiragen Sama (AVSEC) ne suka kama wadanda ake zargin a tashar cikin gida (MMA 1) na filin jirgin.

Tuni dai aka miƙa su ga jami’an hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) domin cigaba da yi musu tambayoyi.

Yayin tuntuɓar mai magana da yawun Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN), Faithful Hope-Ivbaze, ya ce a aiko mana da tambayar ta SMS wacce aka yi. Har yanzu bata amsa saƙon ba.

By Babaji