Bai kamata ana yi wa matan Kannywood kuɗin goro ba – Maryam CTV

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

An ɗan samu lokaci ba a ganin fuskar Jaruma Maryam Sulaiman wato Maryam CTV a wajen aikin fim wanda hakan ya sa mutane suka fara cigiyar ta ko ina ta shiga?

Jarumar da ta yi fice a fitowa a matsayin uwa a gidan manyan masu kuɗi a cikin fim wadda har ake yi mata laƙabin matar manya, ta daɗe ana damawa da ita, kuma har yanzu tauraruwar ta tana haskawa.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Maryam CTV dangane da rashin ganin ta, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Maryam CTV a ‘yan kwanakin nan ba a ganin ki a cikin harkar fim don haka ne ma mutane suka fara tambayar ko ina kika shiga da ba a ganin ki?

MARYAM CTV: To Alhamdulillah, ko da ba a gani na ba na daina harkar ba ne. Ka san kana taka ne Allah yana ya sa, don haka ba na daina harkar fim ba ne, ba kuka hutu na tafi ba. Abin da ya faru ka san kusan shekara kenan na samu karaya a hannu, a lokacin aka yi ɗori na gida, to ashe hannu bai gyaru ba. Wannan ya sa na tafi Nijar aka ɗauki hoton hannun don a tabbatar mini da abin da yake faruwa, wannan kuma ya sa aka gano tsakanin kashi da kashi tsoka ta shiga kuma dole sai an yi mini aiki, to shi ne da na dawo na sake yin shiri na koma, a kalla sai da na yi wata uku zuwa huɗu a Nijar, kuma Alhamdulillah a yanzu sauki ya samu na dawo har na fara ci gaba da aiki.

Ko ya kika ga sauyin rayuwa a zaman jinyar ki?

To rayuwa alhamdulillah Allah ya rufa mini asiri, domin tun kafin na tafi Nijar zaman jinya, ai na yi zaman jinya na shekara guda a nan, kuma Allah ya rufa mini asiri duk abin da nake yi lokacin ina aiki na buƙata ina yin sa a lokacin zaman jinya babu abin da ya canza. 

Kuma da na tafi Nijar zaman jinya a can Yamai na zauna, kuma Ina da aminan arziki a wajen su na zauna na yi jinya, don kulawar da na samu ko a nan garin mu iya abin da za a yi mini kenan.

A yanzu kin samu darasi a zaman jinyar da kika yi ko ya ya kike kallon rayuwa musamman ta fuskar harkar fim?

Ka san ita jarrabawa haka take, kowa da kalar ta sa, don haka da jarrabawa ta zo mini sai na karɓe ta da hannu biyu, domin ita jarrabawa, duk wani mumuni da Allah yake so, sai ya jarrabe shi, don haka na yi wa Allah godiya na karɓi jarrabawar hannu biyu kuma na samu taimakon sa, na samu kulawar jama’a, kuma na samu ɗauki fiye da yadda nake tunani, don haka babu abin da zan ce sai godiyar Allah, haka su ma jama’a da suka ba ni kulawa tsawon shekara guda da na shafe cikin rashin lafiyar nan, Allah ya saka musu da alheri.

 A yanzu dai kin dawo harkar fim gaba ɗaya ?

Haka ne don ka ban daɗe da dawowa ba sai na koma aka tabbatar mini da hannu ya yi kyau. Kuma daman Ina yin fim ɗin, amma dai ba sosai ba, tun da hannu idan bai gyaru ba to ba za a samu yadda ake so ba, domin shi fim ba a zaune ake yi ba, dole ana yi ana motsa hannu, idan ta kama ma a ce ka kai wa wani mari, ko duka, ko ka yi wani abu da zai taɓa hannun, don haka sai na rage na ke yin wanda na san ba zan samu matsala a hannu ba. Amma a yanzu babu abin da ba na yi da hannuna.

Kina cikin mata ‘yan fim da ake ganin masu kwarjini saboda irin rol ɗin da kika fi takawa na ɓabbar mace. Ya kike ganin yanayin mu’amalar ki da jama’a ta wannan fuskar?

Gaskiya Alhamdulillah, masoya na suna nuna mini kauna, kuma mutuntaka da kamala mutum ne yake jawowa kansa duk da yake abu ne daga Allah, amma ita rayuwa yadda mutum ya ɗauki kansa haka mutane za su ɗauke shi, idan kana kiyaye mutuncin ka, sai mutune su gan ka da mutunci, don haka Ina ƙara godiya ga masoya na, don na samu kulawar su ta hanyar addu’o’i da kiran waya  da zuwa har inda nake. Don haka babu abin da zan ce wa masoya sai dai Allah ya saka da alheri. Lokacin da na yi zaman jinya a gidana kullum cika yake da mutane da suke zuwa duba ni. Haka ma zaman da na yi a Yamai na ga tarin masoya, don haka sai godiya da fatan alheri tsakanina da masoya.

Kowa ya sanni ba ni da matsala ko da wani jarumi ko kamfanin shirya fim, don ita rayuwa idan ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi, kuma shi abokin sana’ar ka kamar ɗan uwan ka ne, kuma da na samu kaina a rashin lafiyar nan na san da hakan, domin kafin kowa ya zo kaina a cikin ‘yan uwa na su suka fara tsayawa a kaina, don akwai Sadiya Gyale ita ta fara tsayawa a kaina a asibiti, duk da dai ‘yar uwa ce ta jini, amma hidamar da ta yi mini ko ɗan uwana bai yi mini ba. To saboda haka ni kowa ɗan uwa na ɗauke shi a cikin harkar fim.

Akwai wani kallo da ake yi wa ‘yan fim na cewa ba ku da tarbiyya, ko ya kike ganin wannan maganar?

Wannan shi ne abin da yake ɓata mini rai. Domin ko a gida ɗaya kuka taso, to kowa fa da irin halin sa, wani na kirki wani ba na kirki ba, kuma a haka  nan za a haƙura a zauna , don haka bai kamata ba a rinƙa haɗa wa ana yi mana kudin goro kusan mu manya. Saboda mu dai iya yin mu idan muka ga yarinya ta yi abu ba daidai ba muna ƙoƙarin mu tsawatar mata , idan ka ga mun kawar da kai, sai wadda muka ga ta zo da dutsara, to ka ga wannan ba ji za ta yi ba, to amma bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba.

Don haka ina kira ga jama’a idan an ga mun yi wani kuskure, to kamata ya yi a yi mana nasiha a ja hankalin mu, don mu ma mutane ne kamar kowa, za mu iya yin daidai, kuma za mu iya yin ba daidai ba,  kuma ina ƙara yin godiya ga dukkan masoyana na duniya dangane da irin kulawar da suka ba ni. Allah ya saka wa kowa da alheri.

Madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.

By ukarofi