Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An kashe mutane shida a yankin Akpanya da ke Ƙaramar Hukumar Igala Mela/Odolu a Jihar Kogi lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton daga jihohi makwabta ne su ka mamaye garin.
Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a unguwar Akpanya da ke kan iyakar jihohin Kogi da Enugu.
Majiyar ta bayyana cewa varayin, waɗanda yawansu ya haura 30, sun zo ne a cikin motocin safa, inda suka yi ta harbe-harbe a cikin garin, lamarin da ya sa mazauna garin suka shiga wani mawuyacin hali.
Daily Trust ta tattaro cewa, ba a jima ba da shigowar ‘yan ta’addan garin ba, sai jami’an tsaro, ciki har da ‘yan banga su ka shigo, suka yi artabu da bindiga.
Rikicin da ya biyo baya ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida, daga cikinsu akwai maharan.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi nasarar kwashe gawarwakin mambobinsu guda biyu yayin da suke gudun hijira zuwa jiharsu.
A martanin da ta mayar, gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa ɓatagari da ke shigo wa daga wasu jihohi domin su addabi al’ummar Akpanya sun sa ja zare da ita kuma za su fuskanci fushinta.
Commodore Jerry Omodara (ritaya), mai bai wa Gwamna Yahaya Bello shawara kan harkokin tsaro, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro da ’yan banga ne ya daƙile harin da ‘yan bindigar suka kai a jihar.
Ya ce Gwamna Bello ya bayar da umarnin sake duba sha’anin tsaro gaba ɗaya a yankin domin daƙile hare-haren da haramtacciyar ƙungiyar ke kai wa a nan gaba.
