Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwararsa ta ƙasar Tanzaniya dake ziyarar aiki a ƙasar Sin Samia Suluhu Hassan a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar a ranar 3 ga wannan wata da muke ciki, inda suka sanar da cewa, za su daga matsayin huldar haɗin gwiwa ta sada zumunta bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni dake tsakanin ƙasashen biyu wato Sin da Tanzaniya zuwa wani sabon mataki, haka kuma sun cimma matsaya kan batutuwa da dama, ciki har da kiyaye cudanya da tattaunawa, da haɓaka haɗin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da sauransu.
Ban da haka, shugabannin biyu sun fitar da haɗaɗɗiyar sanarwa, tare kuma da daddale takardun hadin gwiwa da dama, waɗannan suka ƙara kuzari kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Tanzaniya, da ma tsakanin Sin da Afirka a sabon zamanin da ake ciki yanzu.
Shugaba Hassan, ita ce shugabar ƙasashen Afirka ta farko wadda ta kawo ziyara ƙasar Sin, tun bayan da aka kammala babban taron wakilan JKS karo na 20, lamarin da ya nuna cewa, akwai daddaden zumunci tsakanin ƙasar Sin da ƙasar ta Tanzaniya.
Yayin tattaunawar da suka yi, shugaba Xi ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana son samar da sabuwar damar raya ƙasa ga ƙasashen Afirka, kuma tana son ƙara taka rawa wajen nacewa kan manyan ƙa’idojin tafiyar da harkokin ƙasa da ƙasa, da tabbatar da shawarwarin raya duniya, da daga matsayin ƙasashe masu tasowa a cikin harkokin ƙasa da kasa, da kuma ingiza gina kyakkyawar makomar bai ɗaya ga ɗaukacin bil Adama.
Ana iya cewa, kalaman Xi sun bayyana aniyar ƙasar Sin ta ƙara haɓaka haɗin gwiwar dake tsakaninta da Afirka.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa