Daga MAHDI M. MUHAMMAD
’Yan wasan Flamingos sun sauka a Abuja, babban birnin Nijeriya bayan da suka lashe kyautar tagulla a gasar kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekara 17 da aka yi a Indiya.
Nijeriya ta doke Jamus a bugun fenariti bayan da aka tashi 3-3 a wasan neman gurbi na uku a gasar.
Tawagar ’yan wasan ta sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe a ranar Talata inda jami’an hukumar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta NFF suka tarbe su.
Jim kaɗan bayan saukarsu, ministan wasanni da matasa, Sunday Dare, ya gana da ’yan wasan inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta taimaka musu ta yadda za a ƙarfafa tawagar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa Kyaftin ɗin Super Eagles Ahmed Musa, ya bai wa tawagar ’yan wasan kyautar miliyan uku kuma nan take da suka sauka aka ba su cek ɗin kuɗin.
