Daga CMG HAUSA
A jiya ne, aka buɗe bikin baje kolin ƙasa da ƙasa na kayayyakin da ake shigo da su ƙasar Sin karo na biyar (CIIE) a birnin Shanghai.
A jawabin da ta gabatar ta kafar bidiyo yayin buɗe bikin baje ƙolin, babbar darektar ƙungiyar cinikaya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, ƙasar Sin ta zama ƙasar dake kan gaba a duniya wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen ƙetare, kana kasa ta biyu a fannin shigo da kayayyaki da samar da hidima a duniya.
Rawar da ƙasar ɗin take takawa a harkokin cinikayyar ƙasa da ƙasa da ma tsarin kasancewar ɓangarori daban-daban, na da muhimmmanci matuƙa.
Dr Ngozi ta kuma yi nuni da cewa, yadda ƙasar Sin ta halarci taron ministocin ƙungiyar karo na 12 da irin goyon bayan da ta bayar, duk sun haifar da kyakkayawan sakamako.
Ta ce, shirya bikin baje kolin, ya nuna cewa, ƙasar Sin za ta iya taimakawa wajen tabbatar da cewa, harkokin cinikayya sun kasance wani ƙarfi na samun bunƙasuwa da damawa da kowa da kowa.
Don haka, tana fatan yin aiki da ƙasar Sin da sauran mambobin WTO, don gina tsarin kasuwanci mai ƙarfi da inganci a duniya baki ɗaya, da samar da gudummawa ga ɗaukacin bil-Adama da ma duniyarmu.
Mai fassara: Ibrahim
