Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi sun nuna cewa waɗansu mutane da a ke sa ran Lakurawa ne masu da’awar musulunci da ke ƙwace dabbobin mutane musamman shanu da sunan suna karɓar zakka sun kai farmaki a wani ƙauyen Natsini mai tazarar kilomita bakwai tsakanin shi da garin Argungu, inda suka kashe ‘yan sanda biyu da ke aiki a kan babbar hanyar da ta haɗa ƙananan hukumomin Argungu da Augie da kuma Jamhuriyar Nijar sannan kuma suka farwa wani gidan gona mallakar Alhaji Lauwali Abdullahi (Lauwali Black) suka yi awon gaba da shanu da aka kiyasta sun kai 200.
Wani mazauni garin Natsini da bai so a bayyana sunansa ya bayyanawa wakilinmu da cewa maharan sun kai farmaki ne ranar Alhamis ne da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare inda suka harbe ‘yan sanda biyu sannan suka shiga wajen shanun Lauwali Black suka tara shanun sa da kuma na waɗansu fulani da ke maƙotaka da gidan gonar na Lauwali Black suka kora suka ɗauki hanyar Bachaka.
Wakilin mu ya tuntuɓi uban ƙasar Lailaba Alhaji Suleman Muhammad Mera, ya bayyana cewa ba ya da hurumin magana da ‘yan jarida sai dai shugaban ƙaramar hukumar.
Aliyu Sani Gulma shugaban ƙaramar hukumar Argungu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce gaskiya ne an sami iftila’in hari da waɗansu da ake hasashen Lakurawa ne suka kai a ƙauyen Natsini inda bayan sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu kuma suka yi awon gaba da shanu da aka kiyasta sun kai ɗari biyu.
Ya ƙara da cewa tun cikin daren da abin ya faru maigirma gwamna Nasir Idris bai ƙasa a gwiwa ba inda ya umarci duk jami’an tsaro da su fantsama su bi sawun waɗannan mutanen har sai an kama su kuma an ƙwato dukiyar bayin Allah daga hannunsu.
Daga bisani an sami nasarar yi musu luguden wuta inda aka sami nasarar kashe waɗansu da yawa daga cikin su.
Wannan dai shi ne karo na biyu da waɗannan mutanen suka kawo hari a wannan yankin na masarautar Argungu inda ko a watan 11 na shekarar da ta gabata sun kai farmaki a garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie inda suka kashe mutane 17 kuma suka yi awon gaba da shanu masu yawa wanda ya bar baya da ƙura da ya yi sanadiyyar ɓarkewar rikici tsakanin mutanen garin na Mera da Fulanin da ke zaune tare da su da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan Fulani da dama tare da zaman doya da manja.
